Wayar Atiku da Sakataren Gwamnatin Amurka na tsawon mintuna 7 ta bayyana

Wayar Atiku da Sakataren Gwamnatin Amurka na tsawon mintuna 7 ta bayyana

Idan ba ku manta ba, a karshen makon da ya gabata ne Atiku Abubakar wanda yake neman takarar shugaban kasar Najeriya a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP ya amsa waya daga mutanen kasar Amurka.

Wayar Atiku da Sakataren Gwamnatin Amurka na tsawon mintuna 7 ta bayyana
Mike Pompeo ya kira Atiku a waya a Ranar Juma'a da ta wuce
Source: UGC

Tattaunawar da aka yi da ‘dan takarar na PDP ta bayyana fili a halin yanzu bayan mun ji sakon muryar wannan waya da aka yi. Sakataren gwamnatin kasar Amurka watau Mike Pompeo shi ne ya kira Alhaji Atiku Abubakar din a waya.

Wata Sakatariyar Mike Pompeo ce ta kira wayar salular Atiku Abubakar inda Hadiman ‘sa su ka dauka. Bayan ‘yar tattaunawa ne dai su ka mikawa ‘dan takarar wayar domin yayi magana kai tsaye da Sakataren kasar na Amurka.

Mike Pompeo ya fara da gaida Atiku bayan an yi tsawon minti 3 a kan wayar. Pompeo ya fadawa Atiku cewa ya san yana shiryawa zabe (Ranar Asabar) gadan-gadan. A wayar, an ji Atiku da shi Pompeo su na gaida juna su na ta raha.

KU KARANTA: Jam'iyyar SDP za ta marawa Atiku Abubakar baya zaben 2019

Atiku Abubakar yake cewa yana ganin irin kokarin da Sakataren na Gwamnatin Trump yake yi yana mai zagaye kasashen Duniya babu kaukautawa. Atiku ya fadawa Mike Pompeo cewa ya shiryawa zaben tsaf a gidan sa a Adamawa.

Sakataren na kasar Amurka yake cewa su na sa ran ganin an yi zaben kwarai wannan karo kamar yadda shi da kan sa ‘dan takarar yake kira ga jama’a da kuma jam’iyyar sa cewa su guji sayen kuri’un Talakawa da magudin zabe.

A wayar, an ji Alhaji Atiku shi kuma yana yin alkawari cewa zai yi iyaka na sa bakin kokarin na ganin an yi duk abin da ya dace a zaben. Atiku ya kuma fadawa Amurka cewa su kara sa idanu a zaben Najeriya da za ayi wannan karo.

KU KARANTA: Turawan da ke aikin zabe sun ce ana da niyyar dasa bama-bamai

‘Dan takarar ya kuma fadawa Pompeo cewa tun 1999 ake damawa da shi a Najeriya, amma yana ganin cewa wannan zaben ya fi kowane muhimmanci. Mista Pompeo yake cewa ya kira shugaba Buhari yayi masa irin wannan magana.

Mista Mike Pompeo yayi wa Atiku addu’ar Allah ya ba su sa’a tare da ganin cewa zabin jama’a yayi tasiri a zaben da za ayi, shi kuma yayi masa godiya. Sai dai kuma hukumar INEC ta dage zaben a Ranar Juma’an da dare zuwa makon nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Online view pixel