‘Dan Majalisa ya rasa kujerar sa a dalilin satan Burodi a kasar Sulobania

‘Dan Majalisa ya rasa kujerar sa a dalilin satan Burodi a kasar Sulobania

- ‘Dan Majalisa a Kasar Turai ya rasa kujerar sa bayan ya saci Burodi

- Darij Krajcic ya dauki Burodi a shago ya fita ba tare da ya biya ba

- Yayi haka ne don ya iske ma’aikatan shagon su na yi masa yanga

‘Dan Majalisa ya rasa kujerar sa a dalilin satan Burodi a kasar Sulobania

Wani ‘Dan Majalisa ya rubuta takardar murabus saboda ya saci Burodi
Source: Instagram

Mun samu labari cewa wani ‘dan majalisa a kasar Sulobania da ke cikin tsakiyar Nahiyar Turai, ya sauka daga kan kujerar sa, a dalilin satar burodi da yayi a wani shago lokacin da ya je cefane. Gidan jaridar BBC ta rahoto wannan labari.

Darij Krajcic ya rasa kujerar sa ne bayan ya dauki burodi a wani shago a cikin Garin Ljubljana watau babban birnin kasar Sulobania. Wannan ‘dan majalisa yace masu tsaron shagon sun ki kula sa ne lokacin da yake so ya biya kudin

Wannan ‘Dan majalisa, ya fadawa ‘yan jarida cewa ya dauko burodin nan na kwalama mai dauke da ganye da nama watau Sandwich, sai kuma ya iske ma’aikatan shagon su na yi masa yanga a sa’ilin da ya zo da nufin ya sallame su.

KU KARANTA: Saboda in taimaki Yaran Talakawa na shiga siyasa a Najeriya inji Atiku

Mista Darij Krajcic dai ya faki idanun jama’a ya tsere daga shagon ba tare da biyan kudin wannan burodi ba. Sai dai daga baya ne ‘dan majalisar ya dawo da kan sa domin ya biya kayan da ya dauka yana mai bada hakuri cewa a yafe masa.

Babban ‘dan majalisar mai shekaru 54 a Duniya yace ya aikata hakan ne bayan ya bata lokaci ba tare da an mika masa na’urar POS na biyan kudi ba. Wannan ne fa ya sa jam’iyyun adawa su ka huro masa wuta inda shi kuma yayi murabus.

Wannan abu dai ya ba jama’a dariya, amma shi kuwa ‘dan majalisar na jam’iyya mai mulki a kasar Sulobaniya bai dauki lamarin da wasa ba. Krajcic yace ba a san ‘yan jam’iyyar sa da irin wannan abin kunya ba, don haka ya ajiye aiki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel