Yawan kuri’u daga Arewa da Kudu za su tabbatar da nasarar Buhari – Tsohon kakakin majalisar Ekiti

Yawan kuri’u daga Arewa da Kudu za su tabbatar da nasarar Buhari – Tsohon kakakin majalisar Ekiti

Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Ekiti, Hon. Femi Bamisile ya bayyana cewa kuri’u masu dinbin yawa suna jiran dan takaran Shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), shugaban kasa Muhammadu Buhari a yankin Arewa.

Bamisile ya bayyana cewa za’a samu karin kuri’u daga magoya bayansa dake a yankin kudancin kasar don tabbatar da cewa ya lashe zaben shugaban kasa a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Ya zargi ikirarin da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sha yi kan yankin Arewa, inda ya bayyana hakan a matsayin ba komai ba.

Yawan kuri’u daga Arewa da Kudu za su tabbatar da nasarar Buhari – Tsohon kakakin majalisar Ekiti

Yawan kuri’u daga Arewa da Kudu za su tabbatar da nasarar Buhari – Tsohon kakakin majalisar Ekiti
Source: UGC

Dan takaran kujerar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyan APC ya bayyana a jiya cewa jawabi akan sace akwatin zabe da aka alakanta shugaban kasar da shi ya kasance tabbaci akan gaskiyar cewa Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin jam’iyyar APC tare da jajircin shugabancin Buhari za ta yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana da gaskiya.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wasu mutane 3 dauke da na’urar tantance masu zabe a Lagas

A wani lamari na daban, mun ji cewa Dan takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai bari wasu mutane da ake kira da ‘cabal’ su mulki gwamnatinsa ba idan har ya lashe zaben ran Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Atiku, wanda ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduba, yace gaba daya juya gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu ke yi, inda yayi zargin cewa hakan ne ya sanya kasar cikin kangin wahala da wuya da take ciki a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel