Wani matashi ya aika da abokinsa barzahu sakamakon cacar baki akan siyasar Kano

Wani matashi ya aika da abokinsa barzahu sakamakon cacar baki akan siyasar Kano

Duk da irin kiraye kiraye, gargadi da jan hankali wanda Malamai, Iyaye da shuwagabannin al’umma suke yi ga matasa na su kiyayi karkata ga sharrin dake cikin siyasa, amma wasu masu kunnen kashi basa ji, kai sai ka dauka ma a lokacin da ake musu hudubar afkawa ga irin sharrace sharracen nan.

A yayin da zabukan 2019 ke karatowa, manyan yan siyasa sun kebe iyalansu, sun karesu daga shiga duk wata sabgar siyasa ko ta neman takararsu, domin a ganinsu da haka ne kawai zasu tseratar da iyalan nasu, amma suna amfani da yayan talakawa wajen tallatasu.

KU KARANTA: Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Daga tallatawar ne kuma sai labari ya sha bam bam, sai ka fara jin rahoton an kashe mutane kaza a rikicin siyasa, ko kuma an raunata mutane kaza a yayin yakin neman zabe, ko ka ji Yansanda sun cafke yan bangan siyasa kaza, idan ka duba duk yayan talakawa ne.

Anan ma wani shaidan ne yayi ma wani matashi hudubarsa irin ta shaidanu, inda ya kai shi ya baro bayan ya sanya shi burma ma abokinsa wuka a ciki wanda hakan tayi sanadiyyar shekawarsa barzahu babu kakkautawa.

Sai dai abin haushin shine, matashin ya kashe abokin nasa ne saboda bambamcin ra’ayin siyasa, wanda ta kaisu ga cacar baki suna musanta ra’ayin siyasar juna, hakan ne kuma ya harzukasu duka su biyu suka kaure da fada.

Wani ma’abocin kafar sadarwa zamani ta Facebook, Ahmad Deedat ne ya bayyana wannan rahoto inda yace lamarin ya faru ne a kauyen Huguma dake cikin karamar hukumar Takai ta jahar Kano, a ranar Laraba 20 ga watan Febaurairu.

“Musun siyasa ya kaure tsakanin wasu mutane biyu… a yayin da daya ya buga ma abokinsa karfen rodi, shi kuma ya fusata ya daba masa wuka, nan take yace ga garinku nan.” Kamar yadda majiyar Legit.ng ya bayyana.

Idan za’a tuna, a kwanakin baya ne mai martaba Sarkin Kano yayi kira ga shuwagabannin siyasar jahar Kano dasu ji tsoron Allah kadasu jefa jahar cikin rikici saboda biyan bukatarsu, hakan ya biyo bayan hare haren da aka kai ma yan siyasa ne a jahar, daga ciki har da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP Abba K Yusuf wanda aka kona gidansa dake unguwar Chiranchi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel