Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wasu mutane 3 dauke da na’urar tantance masu zabe a Lagas

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wasu mutane 3 dauke da na’urar tantance masu zabe a Lagas

- Jami'an yan sanda sun kama wasu mutane uku dauke da na'urar tantance masu zabe

- An kama mutanen ne a jihar Lagas

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu daga jaridar The Nation ya nuna cewa jami’an yan sanda sun kama wasu mutane uku dauke da na’urar tantance masu zabe na sata a jihar Lagas.

Sai dai zuwa yanzu babu wani cikakken bayani akan wadanda aka kaman.

Labarin na zuwa ne yan kwanaki bayan wata kungiyar damokradiyya, ta Coalition for Clean Polls (CCP), ta zargi hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da gazawa da kuma saba dokokin tarayyar kasar.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wasu mutane 3 dauke da na’urar tantance masu zabe a Lagas

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama wasu mutane 3 dauke da na’urar tantance masu zabe a Lagas
Source: Facebook

Kungiyar ta bayyana cewa hukumar zaben na da wasu gurbatattu a cikinta, mutane masu akidar siyasa sabanin alwashin da ta dauka na kasancewa daga tsakiya.

A wani jawabi dauke das a hannun sakataren labarai na kungiyar ta CCP, Daniel Onche wanda aka aikewa Legit.ng a ranar Talata, 19 ga watan Farairu yace INEC ta nuna cewa ba za ta iya gudanar da zabe na gaskiya da amana kamar yadda take ikirari ba saboda wasu daga cikin jami’anta sun tsunduma kansu a harkar siyasa.

KU KARANTA KUMA: Babu wanda zai mani kawanya idan na hau kujerar Shugaban kasa - Atiku

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Juma'a 22 ga watan Fabrairu 2019 a matsayin ranar hutu domin shirin zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Wannan sanarwar ta fito ne daga ma'aikatan harkokin cikin gida ne a yau Laraba sai dai hutun bai shafi ma'aikatan banki ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel