Babu wanda zai mani kawanya idan na hau kujerar Shugaban kasa - Atiku

Babu wanda zai mani kawanya idan na hau kujerar Shugaban kasa - Atiku

- Dan takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai bari wasu mutane da ake kira da ‘cabal’ su mulki gwamnatinsa ba idan har ya lashe zabe

- Atiku yace gaba daya juya gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu ke yi, inda yayi zargin cewa hakan ne ya sanya kasar cikin kangin wahala da wuya da take ciki a yanzu

- Ya kuma jadadda cewa zai siyar da NNPC domin samar da Karin ci gaba, inda yace a yanzu mutane kalilan ne ke amfana daga ayyukan kadarorin kasar maimakon yan Najeriya baki daya

Dan takarar kujerar Shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya bayyana cewa ba zai bari wasu mutane da ake kira da ‘cabal’ su mulki gwamnatinsa ba idan har ya lashe zaben ran Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Atiku, wanda ya bayyana hakan yayinda yake zantawa da masu ruwa da tsaki daga kananan hukumomi 23 na jihar Kaduba, yace gaba daya juya gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari wasu ke yi, inda yayi zargin cewa hakan ne ya sanya kasar cikin kangin wahala da wuya da take ciki a yanzu.

Babu wanda zai mani kawanya idan na hau kujerar Shugaban kasa - Atiku

Babu wanda zai mani kawanya idan na hau kujerar Shugaban kasa - Atiku
Source: Facebook

Atiku yace ko kadan PDP ba za ta yarda da sace akwatunan zabe ba kuma ba za ta dauki kowani mataki da ya saba doka ba, inda yace bayar da umurnin kashe duk wanda ya sace akwatin zabe ba damokradiyya bane.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi wa manyan sakatarorin gwamnati 12 canje-canjen wurin aiki

Tsohon mataimakin Shugaban kasar yace idan har aka zabe shi a ranar Asabar mai zuwa toh zai siyar da NNPC domin samar da Karin ci gaba, inda yace a yanzu mutane kalilan ne ke amfana daga ayyukan kadarorin kasar maimakon yan Najeriya baki daya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel