Reshe ya juye da mujiya: Yadda aka yi ma wasu jami’an Yansanda fashi da makami

Reshe ya juye da mujiya: Yadda aka yi ma wasu jami’an Yansanda fashi da makami

Rundunar Yansandan jahar Ogun ta sanar da kama wasu miyagun mutane biyu wanda take zargi da yi ma wasu jami’anta guda biyu mata fashi da makami, a ranar Laraba, 20 ga watan Feburairu, inji rahoton jaridar Premium Times.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana haka yayin da yake bajekolin miyagun mutanen a babban ofishin Yansandan jahar dake garin Abekuta, inda ya bayyana sunayen miyagun kamar haka’ Hafiz Omidokun da Peter Babalola.

KU KARANTA: 4+4: Buratai ya kaddamar da bincike akan Sojojin suka bayyana goyon bayansu ga Buhari

Kaakaki Oyeyemi yace yan fashin dake kan babur sun tare Yansandan ne a daidai unguwar Iyana-Ilogbo dake cikin karamar hukumar Ado-Odo, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen aiki, inda yan fashin suka tsaresu, sa’annan suka kwace musu kudade da wayoyin hannu.

“Yansandan suna tafiya ne a cikin motar daya daga cikinsu zuwa wajen aiki, a yayin da suka kai Iyana-Ilagbo sai yan fashin suka tare musu hanya da babur din da suke kai, inda suka nuna musu bindiga suka kwace jakukunansu.

“Sai dai a lokacin da suke kokarin darewa kan baburarsu da nufin tserewa sai Yansandan suka kamasu da fada suna yekuwan neman taimako, ganin haka yasa yan fashin ranta ana kare, amma da taimakon jama’a aka kamasu.

“Jama’a na kokarin kashesu sai wasu jami’an Yansanda a karkashin jagorancin DPO Oyedele Nasiruddeen suka bayyana bayan samun kiraye kiraye daga jama’a game da abin dake faruwa, wanda suka kwaci yan fashin, tare da kwace binidigar dake hannunsu, alburusai da kuma babur.” Inji shi.

Tuni kwamishinan Yansandan jahar, Ahmed Iliyasu ya bada umarnin mika maganan zuwa sashin Yansanda na musamman dake yaki da fashi da makami, wanda aka fi sani da suna F-SARS don cigaba da bincike.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel