An gano yunkurin kona masallatai da kasuwannin Kano lokacin zabe

An gano yunkurin kona masallatai da kasuwannin Kano lokacin zabe

- Wasu masu lura da zaben 2019 sun ce ana shirin kai hari a cikin Kano

- Wata kungiyar kasar waje tace za a nemi a dasa bam a wani Masallaci

- Akwai yiwuwar kuma a kai wani hari a wata kasuwa duk a ranar zaben

An gano yunkurin kona masallatai da kasuwannin Kano lokacin zabe

Masu sa-ido a zaben Najeriya sun ce 'yan daba za su nemi su kai hari a Kano
Source: UGC

Rundunar Malaman zaben da aka aiko Najeriya daga kasar waje a karkashin wata kungiya mai suna Pan African Women Project International Observers ta bayyana cewa akwai shirin da ake yi na tada rikici a Kano a lokacin zabe.

Kungiyar tace labari ya zo gare ta cewa za a nemi a tada bam a wani babban masallacin da ke cikin garin Kano a Ranar Asabar dinnan. Haka zalika, kungiyar tace za a dasa bam a wata kasuwar a ranar da za ayi zaben shugaban kasa.

KU KARANTA: Za a biya Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya albashin watan nan

Kamar yadda labari ya zo mana, Sakatariyar yada labaran wannan kungiya mai suna Misis Mphoeue Keitseng ce ta bayyanawa Duniya wannan a lokacin da tayi hira da wasu manema labarai a cikin garin Kano Ranar Talatar nan da dare.

Wannan Baiwar Allah, Mphoeue Keitseng, wanda ainihin ta ‘yar kasar Botswana ce, ba ta dai bayyana inda ta samu wannan labari ba, amma tace bayanai na liken asiri da su ke zuwa masu, sun tabbatar masu da wannan labari maras dadi.

Kungiyar tayi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara yawan jami’an tsaron da ke jihar Kano domin ganin an yi zabe lafiya. Mphoeue Keitseng tace wasu ‘yan bangar siyasa ne ake so ayi amfani da su domin kai wannan hare-hare a Ranar zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel