Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi kira ga al’ummar Hausawa mazauna unguwar Ikeja ta jahar Legas dasu zabi shugaban kasa Muhammadu Buhar da sauran yan takarkarun jam’iyyar APC a zaben 2019 domin cigaba da cin gajiyar APC.

Osinbajo ya bayyana haka ne yayin taron tattaunawa da Hausawa mazauna Lagos daya gudana a ranar Laraba, 19 ga watan Feburairu a jahar Legas, inda yace akwai wasu tsofaffin shuwagabannin kasar Najeriya da basa son Buhari saboda yana yaki da rashawa.

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa
Source: Twitter

KU KARANTA: 4+4: Buratai ya kaddamar da bincike akan Sojojin suka bayyana goyon bayansu ga Buhari

“Muna fatan ku zabi Buhari a ranar Asabar, mutumin daya tabbatar da gaskiyarsa da rikon amana akan karagar mulki, Najeriya bata da matsalar kudi, sai dai shuwagabannin da aka yi a baya sun sace kudaden ne, amma Buhari ba barawo bane, don haka muke muku aiki da yan kudi kalilan.” Inji shi.

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa
Source: Twitter

Mataimakin shugaban kasa ya bayyana ma mahalarta taron yadda Buhari ke ririta arzikin kasar don amfanin yan Najeriya, inda yace a yanzu Buhari na gina tituna, makarantu, samar da wuta, layin dogo duk da cewa farashin danyen mai ya karye.

“Satar kudin al’umma bashi da addini, akwai kiristoci barayi akwai Musulmai barayi, haka zalika akwai Musulman kirki masu gaskiya, akwai kiristoci masu gaskiya, amma Muhammadu Buhari na daban ne, mutum ne mai gaskiya, hatta mikayansa sun tabbatar da haka.

“Babu shakka idan kuka sake zaben Buhari na a mataki na gaba, yan Najeriya zasu shana, zasu sharbi karin romon dimukradiyya, saboda a yanzu mun sanya tubalin cigaba, kuma kun ga abinda muka yi a harkar sufurin jirgin kasa, tituna da wutar lantarki.” Inji shi.

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa

Osinbajo ya yi kira ga Hausawan Legas su zabi Buhari don cigaba da morewa
Source: Twitter

A jawabinsa, shugaban Hausawa mazauna jahar Legas, Alhaji Ahmed Kabiru ya bayyana jin dadinsa da gayyatar da Osinbajo ya yi musu, inda yace hakan ya nuna yana sane da tasirinsu kenan, sa’annan ya bayyana goyon bayan Hausawan jihohin yarbawa gaba daya ga Buhari da Osinbajo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel