An samu bangaren Jam’iyyar SDP ta goyi bayan Atiku Abubakar

An samu bangaren Jam’iyyar SDP ta goyi bayan Atiku Abubakar

- Wani bangare na Jam’iyyar SDP yana tare da a Atiku Abubakar zaben bana

- ‘Yan Jam’iyyar sun ce Atiku za su zaba bayan wani dogon nazari da su ka yi

- Jam’iyyar adawar tace koke-koken jam’a ya sa ta tsaida ‘Dan takarar na PDP

An samu bangaren Jam’iyyar SDP ta goyi bayan Atiku Abubakar

Atiku zai yi maganin talauci da rashin aikin yi inji Supo Shonibare
Source: Depositphotos

Yayin da ake sauran kwanaki kadan ayi zabe, labari ya kai gare mu cewa an samu wasu ‘yan taware a karkashin jam’iyyar SDP da su ka nuna goyon bayan su ga ‘dan takarar babbar jam’iyyar adawa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Shugaban wani bangare na jam’iyyar ta SDP watau Cif Supo Shonibare, yayi kira ga Magoya bayan sa a jam’iyyar da kuma sauran jama’an Najeriya da su goyi bayan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a zaben da za ayi Ranar Asabar.

KU KARANTA: Jam’iyyar PRP ta zabi ta marawa Shugaba Buhari baya a 2019

Supo Shonibare yake cewa sun yi wa Atiku Abubakar mubaya’a ne a sakamakon yarjejeniyar da jam’iyyun adawar kasar nan da ke karkashin kungiyar CUPP su kayi kwanakin baya bayan dogon nazari game da duk ‘yan takarar.

Shonibare yace jam’iyyar SDP tana cikin tafiyar ta CUPP don haka yace akwai bukatar su goyi bayan mubaya’ar da sauran jam’iyyun hamayya su ka yi wa ‘dan takarar domin ya kaw karshen matsalar rashin aikin yi da talauci.

Bayan duba muradun ‘dan takarar na sauyawa Najeriya fasali da tsari, babban jigon na SDP ya roki al’umma su zabi Atiku Abubakar a Ranar Asabar mai zuwa.Shonibare ya kuma nuna takaicin sa na dage zabe da aka yi a makon jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel