4+4: Buratai ya kaddamar da bincike akan Sojojin suka bayyana goyon bayansu ga Buhari

4+4: Buratai ya kaddamar da bincike akan Sojojin suka bayyana goyon bayansu ga Buhari

Rundunar Sojan kasa ta Najeriya a karkashin jagorancin babban hafsan rundunar, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ta bayyana cewa an janyo hankalinta ga wani hoton wasu Sojoji dake bayyana goyon bayansu ga shugaban kasa Buhari ta hanyar nuna alamar 4+4.

Legit.ng ta ruwaito a daren Laraba ne hotunan Sojojin su hudu suka fara yawo a shafukan sadarwa na zamani suna dauke da bindigu a rataye a wuyansu, sa’annan suka nuna alamar goyon bayan tazarcen Buhari na hudu a tara da hudu, 4+4.

KU KARANTA: 2019: Kodai ku bi umarnin Buhari ko ku ajiye aikinku kafin zabe – Buratai ga Sojoji

4+4: Buratai ya kaddamar da bincike akan Sojojin suka bayyana goyon bayansu ga Buhari

Sojojin
Source: Facebook

Sai dai rundunar ta bayyana yin hakan a matsayin saba ma dokokinta, don haka ta nesanta kanta daga abinda Sojojin nan hudu suka aikata, kuma a yanzu haka ta kaddamar da bincike don gano gaskiyar hoton tare da kamo Sojojin dake ciki.

Kaakakin rundunar, Kanal Sagir Musa yace idan har suka gano akwai kamshin gaskiya a cikin lamarin, zasu hukunta Sojojin dake cikin hoton dukansu kamar yadda dokokin rundunar Sojan kasa ta tanadar.

Daga karshe kaakakin ya tabbatar ma jama’a cewa Janar Buratai ba zai lamunci irin wannan dabi’a da ake zargin Sojojin da aikatawa ba, wanda a lokuta daban daban ya sha gargadin Sojoji game da shiga siyasa tare da daukan bangare a siyasar.

“A duk kiraye kirayen da babban hafsan sojan kasa laftanar janar Tukur Yusuf Buratai yake yi ma Sojoji, ya sha gargadinsu da shiga siyasa ko kuma nuna bangarenci a siyasar, domin kada hakan ya shafi gudanar da aikinsu.” Inji Sagir.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel