Luguden wuta: NAF ta lalata mafakr ‘yan Boko Haram a Borno

Luguden wuta: NAF ta lalata mafakr ‘yan Boko Haram a Borno

Rundunar sojin sama (NAF) ta bayyana cewar dakarun ta da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a karkashin atisayen ofireshon Lafiya Dole sun yi luguden wuta a wani sansanin mayakan kungiyar Boko Haram da ke kauyen Arboko a jihar Borno.

Kakakin rundunar NAF, Ibikunle Daramola, ya ce dakarun soji sun yi kuguden wuta a mafakar ta ‘yan Boko Haram ranar 18 ga watan Fabrairu ta hanyar amfani da jiragen yaki na musamman.

Ya ce sun samu nasarar kai hari mafakar ‘yan ta’addar ne bayan samun bayann sirri.

Sannan ya kara da cewa dakarun NAF sun samu ikon ganin mafakar ‘yan ta’addar ta hanyar amfani da na’urorin da ke cikin jirgin sun a yaki mai suna ISR kuma ba tare da wani bata lokaci ba su ka fara yi ma su luguden wuta. Lamarin da ya yi sanadiyar lalata mafakar tare da kasha da dama daga cikin ‘yan ta’addar.

Luguden wuta: NAF ta lalata mafakr ‘yan Boko Haram a Borno

NAF ta lalata mafakr ‘yan Boko Haram a Borno
Source: Twitter

Daramola ya bayar da tabbacin cewar dakarun sojin sama za su cigaba da aiki tare da takwarorin sun a kasa domin ganin sun lalata dukkan wata mafakar ‘yan ta’adda a yankin arewa ma so gabas.

DUBA WANNAN: Cakwakiya: An kai muhimman kayan aikin zaben Kano jihar Oyo

Ko a jiya, Laraba, sai da Legit.ng ta kawo ma ku labarin cewar rundunar sojin sama (NAF) ta 453 da ke jihar Kauna ta bayyyana cewar ta kama wasu ‘yan bindiga 10 da ake zargi da aikata laifukan ta’addanci tare da kwace shanu 57 daga hannun su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel