Babu aikin fari balle na baki: Yadda jigon PDP ya lakume naira miliyan 350 shi kadai

Babu aikin fari balle na baki: Yadda jigon PDP ya lakume naira miliyan 350 shi kadai

A cigaba da shari’ar tsohon ministan sufurin jiragen sama, kuma kaakakin yakin neman zaben Jonathan a shekarar 2015, Mista Kayode Fayemi, wani shaidan gani da ido ya bayyana a gaban kotu a ranar Laraba, 20 ga watan Feburairu, inda ya tona ma Kayode asiri.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan shaida mai suna Shehu Shuaibu wanda jami’i ne a hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ne, ya bayyana ma kotu yadda Fani Kayode ya karkatar da kimanin naira miliyan dari uku da hamsin ba cas ba as.

KU KARANTA: 2019: Kodai ku bi umarnin Buhari ko ku ajiye aikinku kafin zabe – Buratai ga Sojoji

Babu aikin fari balle na baki: Yadda jigon PDP ya lakume naira miliyan 350 shi kadai

Fani Kayode
Source: UGC

Shehu ya tabbatar ma kotu cewar wannan kudi sun fito ne daga ma’aikatan kula da harkokin kasashen waje, inda suka aika naira miliyan dari takwas zuwa asusun bankin wani kamfani mai suna Joint Trust Dimension Ltd. A ranar 16 ga watan Janairun 2016 ba tare da ya aikata aikin komai ba.

Shuwagabannin kamfanin su uku da EFCC ke tuhuma da sama da fadi da wadannan kudade sun hada da Fani Kayode, tsohuwar ministar kudi Nenadi Usman, Danjuma Yusuf da kuma kamfanin kansa, inda take tuhumatsu da laifuka 17 da suka danganci satan kudin jama’a.

A jawabinsa, Shehu ya bayyana ma kotun cewa mutanen sun yi amfani da kamfanin ne wajen wawuran kudin, inda ya bayyana wasu takardun cire kudi daga banki na bankin Zenith, wanda yace sun ganosu a yayin bincike.

Bugu dsa kari Shehu yayi kokarin bayyana ma kotu wasu karin takardun guda 115 don tabbatar da shaidarsa, amma lauyan wanda ake kara, Norrison Quakers ya nemi a dage sauraron karar har sai ya tabbatar da gaskiyar takardun da Shehu ya bayyana ma kotu ko akasin haka.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu dake cikin shari’ar, sai Alkalin babbar Kotun tarayya dake zamanta a Legas wanda ke sauraron karar ya bada umarnin dage shari’ar zuwa ranar 21 ga watan Feburairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel