Buhari ya yi wa manyan sakatarorin gwamnati 12 canje-canjen wurin aiki

Buhari ya yi wa manyan sakatarorin gwamnati 12 canje-canjen wurin aiki

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya amince da yin canjin wurin aiki ga wasu manyan sakatarori 12 ama’aikatun gwamnatin tarayya.

Sanarwar canje-canjen na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannu Olawunmi Ogunmosunle, darektan sadarwa a ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya(OHCSF), da aka raba ga manema a jiya, Laraba.

Akwai sa hannun shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Winifred Oyo-Ita, a kan takardar.

Jerin manyan sakatarorin da abun ya shafa su ne kamar haka;

Odusote Abimbola; daga ma;aikatar kwadago da daukan aiki zuwa ma’aikatar muhalli.

Istifanus Fuktur; an canja shi zuwa ma’aikatar sadarwa daga ma’aikatar kula da rundunar ‘yan sanda, yayin da aka canja William Ado daga sashen aiyuka na musamman a ofishin sakataren gwamnatin tarayya zuwa ma’aikatar kwadago da daukar aiki.

Buhari ya yi wa manyan sakatarorin gwamnati 12 canje-canjen wurin aiki

Buhari
Source: Depositphotos

Ekaro Chukumuebodo na ma’aikar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya, zai koma ma’aikatar albarkatun ruwa.

Dakta Bukar Wadinga zai koma sashen gama garin aiyuka a ofishin kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya, Mista Kyari Dikwa zai koma sashen aiyuka na musamman, sai kuma uwargida Ajani Olor da za ta koma sashen tsare-tsaren aiyuka dukkan su a ma’aikatar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya.

DUBA WANNAN: Cakwakiya: An kai muhimman kayan aikin zaben Kano jihar Oyo

Mista Umakhihe Afolabi zai koma ma’aikatar kasafi da tsare-tsare, Mista Mbaeri Nnamdi zai koma ma’aikatar kula da rundunar ‘yan sanda, yayin da Mista Babatunde Lawal zai koma sashen ma’aikata a ofishin sakataren gwamnatin tarayya (OSGF).

An mayar da Ininya Festus Daudu sashen aiyuka na musamman a ofishin OSGF, Mista Abel Enitan zai koma ma’aikatar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayyya.

Canje-canjen za su fara aiki ne daga ranar Laraba, 27 ga watan Fabrairu amma a ma’aikatar kasafi da tsare-tsare sai ranar 29 ga watan Maris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel