Tsamo-tsamo: An ga wasu 'yan sanda da sojoji suna yiwa Shugaba Buhari kamfen

Tsamo-tsamo: An ga wasu 'yan sanda da sojoji suna yiwa Shugaba Buhari kamfen

Yayin da ya rage saura kwanaki kadan a gudanar da zabukan da aka dade ana tsimaye a tarayyar Najeriya an ga wasu hotunan jami'an 'yan sanda da na sojoji suna yin ishara da alamar goyon bayan tazarcen shugaba Muhammadu Buhari.

Hotunan dai wadanda suka dauki hankalin jama'a da dama musamman ma a shafukan sada zumunta sun nuna jami'an tsaron ne sun daga hannuwan su duka suna yin nuni da yatsu hudu hudu watau shekarun da shugaba Buhari suke so yayi.

Tsamo-tsamo: An ga wasu 'yan sanda da sojoji suna yiwa Shugaba Buhari kamfen

Tsamo-tsamo: An ga wasu 'yan sanda da sojoji suna yiwa Shugaba Buhari kamfen
Source: UGC

KU KARANTA: Sakataren gudanarwa na PDP yayi murabus

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan alamar dai tuni ake yi mata kallon wata hanya ta nuna goyon bayan ga tazarcen shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda shi ne ya fara yin ta kuma magoya bayan sa ke cigaba da yi.

Sai dai shugabanin hukumomin biyu na sojoji da 'yan sanda dukkan su sun bayyana cewa ma'aikatan su sun soma gudanar da bincike akan hotunan domin tabbatar da sahihancin su kuma da zarar sun kammala za su sanar da matakin su akan jami'an.

Masana dai na ganin bai kamata jami'an tsaron gwamnatin su shiga harkar siyasa ba har ma su nuna goyon bayan su ga wani dan takara domin hakan zai iya gurgunta sahihancin aikin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Online view pixel