Ina rokon ku akan goyon bayan APC a zaben 2019 - Tinubu ya mikawa kabilar Ibo kokon barar sa

Ina rokon ku akan goyon bayan APC a zaben 2019 - Tinubu ya mikawa kabilar Ibo kokon barar sa

- Tinubu ya kirayi 'yan kabilar Ibo da su goyi bayan jam'iyyar APC yayin da babban zaben kasa ke daf da gudana

- Babban jigon na jam'iyyar APC ya kyautata zato na samun nasarar jam'iyyar sa yayin babban zaben kasa

- Tsohon gwamnan jihar Legas ya yi jan kunne na kauracewa duk wata tashin-tashina yayin zabe

Babban jigo na jam'iyya mai ci ta APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya mika kokon sa na bara ga 'yan kabilar Ibo na neman amincewar su da goyon bayan jam'iyyar sa yayin babban zaben kasa da za a gudanar a watan Fabrairu da Maris.

Ina rokon ku akan goyon bayan APC a zaben 2019 - Tinubu ya mikawa kabilar Ibo kokon barar sa

Ina rokon ku akan goyon bayan APC a zaben 2019 - Tinubu ya mikawa kabilar Ibo kokon barar sa
Source: Facebook

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Kanwa Uwar gamin matsalolin jam'iyyar ta APC ya yi wannan kira ne yayin taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar sa da aka gudanar a yau Laraba cikin birnin Ikeja na jihar Legas.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta gudanar da wannan babban taro domin tumke damarar ta tare da zage dantse domin tabbatar da shirin ta na babban zaben kasa da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu da kuma 9 ga watan Maris na 2019.

Tinubu ya ce gwamnatin jam'iyyar APC ta sauke nauyin al'ummar yankin Kudu maso Gabashin kasar nan da ya rataya a wuyanta ta fuskar tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya ba tare da nuna masu wariya ba.

KARANTA KUMA: 'Yan ta'adda sun hallaka babban soja da Mutane 6 a jihar Katsina

Tinubu wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Legas ya kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar sa ta sauke duk wani nauyi na al'umma da rataya a wuyan ta ba tare da duba ya zuwa bambanci ga baki ko masu cirani a cikin ta.

Yayin da yake ci gaba da neman goyon bayan 'yan kabilar Ibo, Tinubu ya ce gwamnatin jam'iyyar APC ta bai wa dukkanin al'ummar yankin Kudu maso Gabashin kasar nan hakkokin su musamman ta fuskar habakar harkokin su na kasuwanci da tattalin arziki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel