Zabe: Gwamnatin tarayya ta bayyana Juma'a a matsayin ranar hutu

Zabe: Gwamnatin tarayya ta bayyana Juma'a a matsayin ranar hutu

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Juma'a 22 ga watan Fabrairu 2019 a matsayin ranar hutu domin shirin zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Wannan sanarwar ta fito ne daga ma'aikatan harkokin cikin gida ne a yau Laraba sai dai hutun bai shafi ma'aikatan banki ba.

Zabe: Gwamnatin tarayya ta bayyana Juma'a a matsayin ranar hutu

Zabe: Gwamnatin tarayya ta bayyana Juma'a a matsayin ranar hutu
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Sanarwar ta ce, "Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Juma'a 22 ga watan Fabrairun 2019 a matsayin ranar hutu sai dai hutun bai shafi wadanda ke gudanar da muhimman ayyukan ba da masu aikin banki,"

"An bayar da hutun ne domin al'ummar kasa su samu damar komawa garuruwan da za su kada kuri'unsu sakamakon dage zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisun tarayya.

"An umurci hukumomin tsaro su tabbatar da tsaro da lafiyar al'umma gabanin zabe, lokacin zabe da bayan zabe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel