Cakwakiya: An kai muhimman kayan aikin zaben Kano jihar Oyo

Cakwakiya: An kai muhimman kayan aikin zaben Kano jihar Oyo

An samu rudani a yau, Laraba, a babban bankin kasa (CBN) reshen jihar Oyo da ke Ibadan bayan an samu takardar hukumr zabe mai zaman kan ta (INEC) mai lamba EC8B mallakar jihar Kano.

Takardar, wacce na daga cikin muhimman kayan aikin zabe, ta wata mazaba ce a jihar Kano

Wasu ma’aikatan INE ne su ka fara kula da wannan kuskure yayin da su ka je CBN domin karba tare da ware muhimman kayan aikin zabe da aka kawo jihar ta Oyo.

Lamarin ya faru ne a gaban manema labarai da aka gayyato domin shaida karba da kuma ware muhimman kayan aikin zabe kamar yadda INEC ke yi a kowacce jiha.

Kano kuma!”, ma’aikatan su ka fada cikin mamaki yayin da wata mata ta dauko takardar.

Cakwakiya: An kai muhimman kayan aikin zaben Kano jihar Oyo

Jirgin rundunar sojin sama yayin jigilar muhimman kayan aikin zabe
Source: Facebook

Daga bisani daya daga cikin ma’aikatan ya dauki takardar zuwa wurin wani babban jami’in INEC, wanda ya karbi fom din din tarer da yin wani rubutu a wata rijista.

Da manema labarai su ka tambayi babban jami’in hukumar INEC da ya karbi fom din a kan ko ya ya za a yi da shi, sai ya ce; “za mu bawa CBN domin ta mayar da shi jihar Kano cikin gaggawa.”

DUBA WANNAN: Satar akwati: Dole mu bi umarnin Buhari – Buratai ya mayar wa Atiku martini

Da aka sake tambayar shi ko akwai ragowar wasu muhimman kayan aikin zaben mallakar jihar Kano, sai ya amsa da cewar; “ya zuwa yanzu dai shi kadai mu ka samu.

Kokarin jin ta bakin shugaban sashen yada labarai na INEC a jihar Oyo, Mista Olayiwola Arowolo, a kan lamarin bai samu ba bayan be amsa kiran waya da aka yi ma sa ba.

Kazalika, kwamishinan INEC na jihar, Mista Mutiu Agboke, bai amsa sakon da manema labarai su ka aika ma sa a kan lamarin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel