Makiyaya sun hallaka Mutane 16 a jihar Benuwe

Makiyaya sun hallaka Mutane 16 a jihar Benuwe

Da sanadin shafin jaridar The Nation mun samu rahoton cewa, ana zargin wasu makiyaya sun salwantar da rayukan kimanin Mutane 16 tare da raunata Mutane biyu yayin zartar da wani mummunan hari a karamar hukumar Agatu ta jihar Benuwe.

A yayin aukuwar wani mummunar hari na makiyaya a yau Laraba cikin kauyen Ebete na gundumar Usha da ke karkashin karamar hukumar Agatu ta jihar Benuwe, rayukan kimanin Mutane 16 sun salwanta tare da jikkatar Mutane biyu.

Makiyaya sun hallaka Mutane 16 a jihar Benuwe

Makiyaya sun hallaka Mutane 16 a jihar Benuwe
Source: Depositphotos

Kafar watsa labarai ta jaridar The Nation ta ruwaito cewa, makiyaya sun zartar da wannan mummuna hari cikin kauyen Ebete da misalin karfe 1 na daren yau Laraba yayin da al'umma ke ribatar dare da ake ma sa lakabi da Mahutar Bawa.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, wadanda suka raunata yayin aukuwar mummunan harin na ci gaba da samun kyakkyawar kulawa a wani babban asibiti da ke yankin Obagaji a karamar hukumar Agatu.

KARANTA KUMA: Sayar da kamfanin Man Fetur na NNPC ba bu gudu ba bu ja da baya muddin na hau Kujerar mulki - Atiku

Babban jami'in soji dake jagorancin aikin sintiri da tabbatar da zaman lafiya a jihar Benuwe, Manjo Janar Adeyemi Yekini, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari. Kazalika gwamnan jihar, Samuel Ortom, ya bayyana takaicin sa tare da yin tur gami da Allah wadai.

Gwamna Ortom da sanadin babban sakataren sadarwa na fadarsa, Iterver Akase, ya kuma nemi hukumomin tsaro da su sake zage dantse wajen sauke nauyin da rataya a wuyan su domin tseratar da rayuka da kuma dukiyoyin al'umma a jihar Benuwe.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel