Dalilin da yasa kasar Iran ke goyon bayan Atiku - SGN

Dalilin da yasa kasar Iran ke goyon bayan Atiku - SGN

Kungiyar Sunnah a Najeriya, SGN, ya bayyana dalilin da yasa kasar Iran ke marawa dan takaran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Atiku Abubakar, baya a zaben da za'a gudanar ranan Asabar, 23 ga watan Febrairu.

Shugaban Da'awan kungiyar, Muntaka Kafinsoli, ya bayyana cewa hadakar Atiku d ayan kungiyar akidar Shia yasa kasar Iran ke son ya lashe zaben. Game da cewarsa, Atiku na amfani da rikice-rikicen da suka faru tsakanin hukuma da Shi'a wajen neman goyon bayansu.

Kungiyar ta kara da cewa Atiku ya samu kudade daga kasar Iran a kwanakin da suka gabata domin yakin neman zabensa.

Yace: "Atiku na amfani da harkan tsaro wajen jawo hankalin yan Shi'a da muguwar akidarsu domin samun nasara a zabe. Yana neman goyon bayansu yaci zabe sannan ya saki mambobinsu dake tsare."

"Dukkanmu mun san yan Shi'a rikice-rikicen da suke kawowa tsaro a Najeriya. Saboda haka, duk wanda ke kokarin goyon bayansu tamkar abokin tarayyansu ne. Saboda haka muna kira ga jami'an tsaro su gudanar da bincike kan al'amarin."

"Yana samun kudi da wasu kayayyaki daga kasar Iran a yanzu haka domin isar da muradun yan Shia a Najeriya da kuma Iran. Wannan ya sabawa yancin kasa da mutuncinta."

Za ku tuna cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta sanya wando daya da mabiya akidar Shi'a tun shekarar 2015 da suka samu sabani da babban hafsan sojin Najeriya, Tukur Buratai.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel