An kai wa tawagar dan takarar sanata a APC hari

An kai wa tawagar dan takarar sanata a APC hari

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta tabbatar da kai hari a kan tawagar dan takarar kujerar sanata a jam’iyyar APC, Lola Ashiru, a garin Ojoku da ke karamar hukumar Irepodun.

Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin ta na jihar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya raba wa manema labarai yau, Laraba, a Ilorin.

Sanarwar ta kara da cewa tuni kwmishinan ‘yan sanda a jihar Kwara, Kayode Egbetokun, ya tura Karin jami’an ‘yan sanda zuwa garin Ojoku bayan samun rahoton kai harin da yammacin jiya, Laraba.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar Ashiru ne dan takarar kujearar sanatan jihar Kwara ta kudu.

An kai wa tawagar dan takarar sanata a APC hari

An kai wa tawagar dan takarar sanata a APC hari
Source: UGC

Tawagar jami’an rundunar ‘yan sanda karkashin jagorancin DPO Ilemona sun shawo kan rikicin da ya barke tare da yin nasarar tserar da dan takarar ba tare da samun ko kwarzane ba.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta tabbatar da kai hari a kan al’ummar Agatu

“An kama wasu daga cikin wadanda su ka kai harin, kuma an kwantar da rikicin da ya tashi a wurin yakin neman zaben.

“Jami’an mu sun shiga farautar ragowar wadanda su ka gudu daga cikin ‘yan ta’addar yayin da mu ke cigaba da gudanar da bincike a kan afkuwar lamarin,” a cewar jawabin rundunar ‘ayn sanda.

Rundunar ‘yan sandan ta jaddada aniyar ta na kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar Kwara.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel