Sayar da kamfanin Man Fetur na NNPC ba bu gudu ba bu ja da baya muddin na hau Kujerar mulki - Atiku

Sayar da kamfanin Man Fetur na NNPC ba bu gudu ba bu ja da baya muddin na hau Kujerar mulki - Atiku

A yau Laraba, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayin halartar zaman sauraron ra'ayin al'umma a jihar Kaduna, ya sake jadadda matsayar sa ta yadda zai yi da kamfanin man fetur na NNPC muddin ya hau kujerar mulkin kasar nan.

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu cewa, dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya sake tabbatar da shirin sa na sayar da kamfanin man fetur na kasa wato NNPC, bayan samun nasarar sa a babban zaben kasa na ranar Asabar, 23, ga watan Fabrairun 2019.

Atiku ya ce yana nan akan bakan sa na ba bu gudu ba bu ja da wajen sayar da kamfanin man fetur na kasa muddin ya yi nasara a zaben kujerar shugaban kasa da za a gudanar a wannan mako. Sai dai Atiku ya ce ba ya da nufin sayar da kamfanin ga abokanan huldar sa.

Sayar da kamfanin Man Fetur na NNPC ba bu gudu ba bu ja da baya muddin na hau Kujerar mulki - Atiku

Sayar da kamfanin Man Fetur na NNPC ba bu gudu ba bu ja da baya muddin na hau Kujerar mulki - Atiku
Source: Depositphotos

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Atiku ya yi furucin hakan a yau Laraba yayin zaman sauraron ra'ayin dukkanin rassa na shugabannin jam'iyyar sa ta PDP da aka gudanar cikin filin cinikayyar kasa da kasa na baja koli da ke jihar Kaduna.

A yayin zayyana dalilai na rashin cin moriya ko rashin samun wata riba da talakawan kasar nan ke yi, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, kamfanin man fetur na NNPC ya gaza taka wata muhimmiyar rawar gani daidai da dalilai na manufofin assassa shi tun a shekarar 1977.

A cewar Wazirin Adamawa, sayar da kamfanin NNPC da sauran matatun man fetur uku shine ka-in-da-la-in wajen ribatuwar kasar nan tare da buga misali dangane da yadda ta kasance wajen sayar da kamfanin sadarwa na Najeriya wato NITEL.

KARANTA KUMA: Hotuna: Jiragen sama na gwamnatin jihar Akwa Ibom sun iso birnin Uyo

Baya ga kasancewar Najeriya cikin jerin kasashen duniya da ke sahun gaba ta fuskar arzikin man fetur, Atiku cikin takaici ya bayyana yadda kawowa yanzu kasar nan ke ci gaba da sayo tataccen man fetur daga kasashen ketare tare da sayar da shi akan farashi mai tsadar gaske a cikin ta.

Dan takarar kujerar shugaban kasa a babbar adawa ta kasar nan ya kara da cewa, muddin aka zabe shi a matsayin jagoran kasar, zai sayar wa da al'ummar Najeriya kamfanin NNPC kamar yadda tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya yiwa babban kamfanin sadarwa na NITEL.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel