Ikon Allah ne kada zai iya hana zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu – Shugaban INEC ga kasashen duniya

Ikon Allah ne kada zai iya hana zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu – Shugaban INEC ga kasashen duniya

- Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, yace “wani kudiri na Allah ne kadai zai iya hana gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki

- Hukumar zabe dai ta dage zaben wanda ya kamataa gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu

- Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar bata da wani dalili da take ganin cewa wani abu zai daktar da zaben ranar Asabar mai zuwa

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, Farfesa Mahmood Yakubu, yace “wani kudiri na Allah ne kadai zai iya hana gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka dage za a yi a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu.

Shugaban na INEC ya bayyana hakan a Abuja yayinda yake jawabi ga wani taron diflomasiyya da kungiyar masu sanya idanu a zabe na kasashen duniya a Najeriya.

Ikon Allah ne kada zai iya hana zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu – Shugaban INEC ga kasashen duniya

Ikon Allah ne kada zai iya hana zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu – Shugaban INEC ga kasashen duniya
Source: Instagram

Ma’aikatar kula da harkokin waje ce ta shirya taron tare da hadin gwiwar INEC domin tattaunawa tare da abokai da kuma takwarorin Najeriya kan zaben da aka dage.

Yakubu wanda ya samu wakilcin wani kwamishinar INEC, Dr Mustapha Lecky ya bayyana cewa hukumar ta tanadi komai domin tabbatar da gudanr da zaben a ranar Asabar.

Shugaban INEC ya bayyana cewa hukumar bata da wani dalili da take ganin cewa wani abu zai daktar da zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Zabe: Akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a Kano – Kungiyar masu sa ido a zabe

Yace hukumar ta shirya wasu ajanda shida da take ganin ya kamata ayi domin tabbatar da nasarar zabe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel