Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina ta bayyana cewa ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane a jihar Katsina.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Gambo Isah ne ya sanar da hakan a wata takardar manema labarai da jami’in ya saki anar Laraba, 20 ga watan Fabrairu a garin Katsina.

Dan ta'addan ya yi wa wani dan kasuwa barazanar cewa zai yi garkuwa da shi, in har bai biya Naira miliyan biyu ba, mutumin mai suna Magaji Gudaji mai shekaru 30, wanda ke zama a kauyen ‘Yandoka dake Dayi a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina

Yan sanda sun kama kasurgumin mai garkuwa da mutane a Katsina
Source: UGC

Yan sandan sun yi nasarar kama shi ne bayan da suka samu wasu bayanai na sirri, inda suka same shi da wayar hannu kirar Itel da kuma layin wayar da yake amfani da shi wajen aikata ta'addanci, rundunar ta ga sakon barazanar da ya aike wa da wancan dan kasuwan, sannan kuma tuni ya amsa laifin nashi ma.

KU KARANTA KUMA: Kwankwaso yana so a harbe masu karya allon takarar PDP a Kano

Rundunar ta ce da zarar ta kammala binciken ta za ta gurfanar da mutanen a gaban kotun don fuskantar hukuncin da ya dace da shi, sannan tana ci gaba da aikin gano sauran abokan ta’asar sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel