Rundunar soji ta tabbatar da kai hari a kan al’ummar Agatu

Rundunar soji ta tabbatar da kai hari a kan al’ummar Agatu

Kwamandan rundunar soji ta musamman ‘Operation Whirl Stroke’ da ke aikin atisaye a jihar Benuwe ya tabbatar da cewar an kai hari a kan al’ummar garin Agatu da sanyin safiyar yau, Laraba.

A jawabin da Manjo Janar Adeyemi Yekini ya fitar, ya ce ya zuwa yanzu rundunar soji ba ta da kididdigar adadin mutanen da su ka rasa tare da bayyana cewar an aika tawagar soji zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewar aikin rundunar ‘Operation Whirl Stroke’ shine kakkabe ‘yan ta’adda daga jihohin Benuwe, Nasarawa da Taraba.

Na samu labari yau, da rana, cewar wasu ‘yan bindiga sun kasha mutane a garin Agatu.

Rundunar soji ta tabbatar da kai hari a kan al’ummar Agatu

Rundunar soji
Source: UGC

“Ba ni da tabbacin adadin mutanen da su ka mutu amma ban a jin sun kai mutane 16. Mun tura tawagar soji da za ta ke gudanar da sintiri a yankin da abun ya faru.

DUBA WANNAN: Satar akwati: Dole mu bi umarnin Buhari – Buratai ya mayar wa Atiku martini

“Yankin da abun ya faru ya na jihar Benuwe ne amma ya fi saukin shiga ta jihar Nasarawa. Mun aika tawagar sojoji domin tabbatar da gaskiyar abinda ya faru,” a cewar Yekini.

Agatu da ragowar wasu sassan jihar Benuwe sun dade sun a fuskantar matsalar hare-haren ‘yan bindiga, musamman a ‘yan shekarun baya bayan nan. Mutanen yankin na dora alhakin kai hare-haren a kan makiyaya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel