2019: Shugaban kasa Buhari ne zabin mu - Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya

2019: Shugaban kasa Buhari ne zabin mu - Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya

- Kwanaki kadan gabanin babban zaben kasa kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya ta bayyana goyon bayan ta akan shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Jagoran kungiyar, Aminu Goroyo, ya ce kungiyar ta yanke shawarar hakan bayan samun amincewar dukkan rassan ta da ke jihohi 36 a fadin kasar nan

- Kungiyar RIFAN, ta kirayi daukacin al'ummar Najeriya da su yi tururuwa wajen tabbatar da nasarar shugaban kasa Buhari yayin babban zaben kasa a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu

Gabanin babban zaben kasa na ranar Asabar, kungiyar manoman shinkafa ta Najeriya, Rice Farmers Association of Nigeria, RIFAN, ta bayyana goyon bayan ta ga dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Muhammadu Buhari.

2019: Shugaban kasa Buhari ne zabin mu - Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya

2019: Shugaban kasa Buhari ne zabin mu - Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya
Source: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kungiyar ta yanke wannan babban hukunci na goyon bayan shugaban kasa Buhari a jiya Talata cikin garin Abuja bayan samun amincewar dukkanin rassanta da ke jihohi 36 a fadin kasar nan.

Shugaban kungiyar RIFAN, Aminu Goroyo, ya bayar da shaidar cewa dukkanin mambobin kungiyar kimanin miliyan 12.2 da ke fadin Najeriya sun bayyana kudirin su da aminci na goyon bayan shugaban kasa Buhari yayin babban zabe na ranar Asabar.

Kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito, kungiyar RIFAN ta bayyana cewa, goyon bayan ta ga shugaban kasa Buhari ya bayu ne a sakamakon daurin damarar sa kan akidu na habaka tattalin arzikin kasar nan ta hanyar bai wa harkokin noma muhimmancin gaske.

KARANTA KUMA: Ina da tabbacin za a gudanar da zabe na gaskiya da adalci - Buhari

Goroyo ya bayyana cewa, sake zaben Buhari domin tabbatar da nasarar sa ta tazarce a bisa kujerar mulki zai yi tasirin gaske ta fuskar wadatuwar abinci da amfanin noma cikin kasar nan tare da saukaka dogaro akan arzikin man fetur da ma'adanan sa.

Jagoran kungiyar RIFAN ya kara da cewa, kyawawan akidu gami da tsare-tsaren Buhari akan harkokin noma zai yi tasiri wajen fidda kasar nan zuwa tudun tsira ta fuskar kawo karshen barazanar rashin aikin yi, fatara, yunwa da kuma karancin abinci.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel