Satar akwati: Dole mu bi umarnin Buhari – Buratai ya mayar wa Atiku martini

Satar akwati: Dole mu bi umarnin Buhari – Buratai ya mayar wa Atiku martini

Shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce kundin tsarin mulkin kasa ya wajabta wa rundunar soji yin biyayya ga umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, tare da yin watsi da kiran da Atiku ya yi wa rundunar soji na ta yi watsi da umarnin Buhari a kan ma su satar akwatin kuri’u lokacin zabe.

A ranar Litinin ne shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro da kar su tausaya wa duk wanda ya yi yunkurin sace akwati yayin zabukan da za a gudanar.

Da ya ke mayar da martini, Atiku, dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, ya ce umarnin da Buhari ya bayar ya saba da tanadin dokokin Najeriya tare da yin kira ga rundunar soji da su yi watsi da umarnin da Buhari ya bayar.

Da ya ke Magana yayin gana wa da manyan jami’an rundunar soji a yau, Laraba, Buratai ya bayyana cewar abun mamaki ne a ce mutumin da ke neman zama shugaban kasa zai yi kokarin tunzura rundunar soji.

Satar akwati: Dole mu bi umarnin Buhari – Buratai ya mayar wa Atiku martini

Buratai
Source: UGC

Duk da bai ambaci sunan Atiku ba, a bayyane ta ke cewar yana mayar da martini ne gad an takarar na jam’iyyar PDP.

Da ya ke jaddada sakon Buhari, Buratai ya ce duk wanda ya yi kokarin kawo cikas yayin zabe tabbas zai dandana kudar sa.

Daga cikin tanade-tanaden dokar aikin soja akwai yin biyayya ga shugaba mai iko. Abun takaici ne a ce mai neman zama shugaban kasa na tunzura rundunar soji ta yi rashin da’a.

DUBA WANNAN: Atiku ya lissafa jihohin arewa 3 da ake shirin sake daga zabe

“Mun sha bayyana cewar babu ruwan soja da harkokin siyasa. Sai dai, rundunar soji ba za ta lamunci duk wani yunkuri na tunzura ta domin dalilan siyasa ba.

“Ina mai kira ga ma su irin wannan furuci da su janye kalaman su. Zan sake fada domin warware duk wani shakku; rundunar soji na aiki ne bisa kware wa da bin doka. An gina rundunar soji ne a kan tubulin da’a, hakan ne kuma ke rike da rundunar. Dole biyayyar soja ta kasance dari bisa dari. Za mu yi wa Najeriya da jama’ar ta aiki bisa tsarin doka da oda,” a cewar Buratai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel