Dalilin da yasa DSS ta soke gayyatar da ta yi wa jami’an INEC

Dalilin da yasa DSS ta soke gayyatar da ta yi wa jami’an INEC

A ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu ne hukumar tsaro ta DSS, ta dakile gayyatar da ta yi wa wasu manyan jami’an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) zuwa hedikwatar hukumar da ke Abuja.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an gayyaci babban jami’i Okechukwu Ibeanu tare da wasu jami’ai hudu domin su je su bayar da bayani game da dalilin da ya kawo dage zabe.

An tattaro cewa jami’an INEC da aka gayyata, duk ta wayoyin su ne aka kira su daya bayan daya ana sanar da su gayyatar da kuma lokacin da za su je din, karfe daya na ranar jiya Talata.

Sai dai kuma daga bisani hukumar suka soke kiran da suka yi wa jami’an zaben.

Dalilin da yasa DSS ta soke gayyatar da ta yi wa jami’an INEC

Dalilin da yasa DSS ta soke gayyatar da ta yi wa jami’an INEC
Source: UGC

Kamar yadda aka kira su daya bayan daya aka shaida musu gayyatar, haka aka sake kiran su da guda-guda ana sanar da su cewa an soke gayyatar da aka yi musu, ba sai sun kai kan su ba.

Amma kuma Shugaban hukumar zabe, Farfesa Mahmood Yakubu ya shaida wa manema labarai cewa DSS ba su gayyaci ko da jami’in zabe guda daya ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan Shi’a na zanga-zanga a ma’aikatar harkokin waje

Ya bayyana haka ne, duk kuwa da cewa DSS sun shaida wa wadanda aka gayyata din cewa sun sanar da Shugaban INEC gayyatar da suka yi wa jami’an na sa biyar.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin din ce dai Buhari ya ce zai sa a binciki dalilin da ya sa aka dage zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel