Da dumi-dumi: Na hannun daman Buhari da wasu da dama sun koma jam’iyyar PDP

Da dumi-dumi: Na hannun daman Buhari da wasu da dama sun koma jam’iyyar PDP

Ana saura kwanaki uku kafin ranan zaben kasa, jam’iyyar PDP reshen Sokoto tayi babbar kamu a lokacinda Alhaji Muhammad Gobirawa, mataimakin Shugaban yan fansho na Najeriya a yankin Arewa maso yamma kuma babban magoyin bayan kungiyan Buhari Support Organisation (BSO) mai taken “Buhari Sak” a Sokoto ya sauya sheka daga jam’iyyar APC.

Gobirawa Wanda a halin yanzu ke rike da mukamin mataimakin shugaban kungiyar Aminu Waziri Tambuwal (AMATA) ya ayyana wa manema larai a Sokoto a ranar Laraba cewa ya zama dole shi da mutanensa dake kungiyar BSO su sauya sheka saboda suna da yakinin cewa PDP ce jam’iyyar siyasa mai cikakkiyar alkawari kuma tana dauke da alamu dake nuna cewa damokardiyya zata dawo Najeriya.

Da dumi-dumi: Na hannun daman Buhari da wasu da dama sun koma jam’iyyar PDP

Da dumi-dumi: Na hannun daman Buhari da wasu da dama sun koma jam’iyyar PDP
Source: Depositphotos

A cewar shi, yayi amfani da wannan daman ne don bayyana wasu dalilai akan sauya shekarsa, yace ya kamata ya bayyanawa mutanen jihar kuma ko shakkan cewa “a matsayina na dan Najeriya mai cikakkiyar hankali, Ina iya yanke shawara akan kowace jam’iyya da na ga daman shiga ba tare da danganta mataki da na dauka da iyalina ba.”

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku na da alaka da yan Shi’a – Kungiyar Sunnah

Gobirawa har ila yau, ya bukaci al’umma dasu mayar da hankali akan al’amura ba tare da ajiye juna a a zuciya ba kamar yanda damokardiyya ta tanadar, inda dan kasa yake da damar bayyana ra’ayinsa.

Yace kungiyar shi ta mayar da hankali don ganin PDP ta cimma nasara tare da sake zabar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a karo na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel