Da duminsa: Atiku ya samu goyon bayan wata 'yar takarar shugaban kasa

Da duminsa: Atiku ya samu goyon bayan wata 'yar takarar shugaban kasa

Labarin da muke samu yanzu na nuni da cewa 'yar takarar shugaban kasa krkashin jam'iyyar National Interest Party (NIP) Eunice Atuejide ta hakura da takararta, inda ta goyi bayan dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Ita ce mace ta biyu da ta janye takararta ta shugabancin kasar bayan Oby Ezekwesili ta jam'iyyar ACPN, sakamakon samun sabani da shuwagabannin jam'iyyar, da kuma rikicin cikin gida da ya mamaye jam'iyyar.

Atuejide, a cikin wata sanarwa a shafinta na Twitter, ta bayyana cewa ta zabi goyon bayan Atiku ne saboda daukar tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, a matsayin abokin takararsa.

KARANTA WANNAN: Buhari bai yi kuskure ba, wanda ke son ransa ya guji satar akwatin zabe - Festus Keyamo

Da duminsa: Atiku ya samu goyon bayan wata 'yar takarar shugaban kasa

Da duminsa: Atiku ya samu goyon bayan wata 'yar takarar shugaban kasa
Source: Twitter

- Ta ce: "Na za bi na yi yaki akan ci gaban kowanne dan Nigeria ta bangaren Alhaji Atiku Abubakar. Ba zan iya kare PDP na mulkin kama karya a tsakanin 1999 zuwa 2015 ba amma duk da hakan ba zan iya kare kaina daga ganin laifin APC na aikata laifi fiye da na PDP ba.

"Kuma, walau muna kiransu PDP, APC, PPA, ANN, YPP ko NIP, dukanmu dai mutane daya ne dage sauya sheka daga wannan jam'iyyar siyasar zuwa wata domin nemawa kawunanmu matsugunni da kuma bakin fada a ji.

"A tawa mahangar, ba wai jam'iyya ba ce abuda jama'a ya kamata su rinka dubawa, ko dai Ahaji Atiku Abubakar a karkasin PDP ko kuma shugaban kasa Buhari a karkashin APC.

"Ina so na bayyana matsaya ta a fili, daga yanzu, na koma goyon bayan Atiku karkashin jam'iyyar PDP."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel