2019: Kodai ku bi umarnin Buhari ko ku ajiye aikinku kafin zabe – Buratai ga Sojoji

2019: Kodai ku bi umarnin Buhari ko ku ajiye aikinku kafin zabe – Buratai ga Sojoji

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya gargadi Sojoji game da muhimmancin yi bin doka da oda da kuma bin umarnin na gaba a aikin Soja, musamman idan babban kwamanda ya basu umarni, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Buratai ya yi kira ga dukkanin Sojojin Najeriya walau karamin Soja ko hafsan Soja dasu tabbata suna masu biyayya ga gwamnatin tarayy, idan kuma suna shakkar biyayyarsu toh su ajiye aiki zuwa ranar Juma’a, 22 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Labari cikin hotuna: Taron majalisar zartarwa a karkashin jagorancin Buhari

2019: Kodai ku bi umarnin Buhari ko ku ajiye aikinku kafin zabe – Buratai ga Sojoji

Buratai da Buhari
Source: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Buratai ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin da yake ganawa da manyan kwamandojin rundunar Sojan kasa a shelkwatar rundunar Sojan kasa dake babban birnin tarayya Abuja.

“Ginshikin aikin Soja shine ladabi da biyayya, kuma idan har babu biyayya, aikin Soja ba zai yiwu ba, daga cikin ginshikanmu akwai biyayya ga hukuma, dole ne biyayyarka ta kasance cikakkiyar biyayya dari bisa dari.

“Idan har akwai wani Soja da yake jin shakku a ransa game da biyayya ga Najeriya kamar yadda take a yanzu, toh yana da daga nan har zuwa ranar 22 ga watan February domin ya yi murabus daga aikin Soja, ba zamu lamunci rashin kunya da kin bin doka da oda a rundunar Sojan kasa ba.” Inji shi.

Haka zalika Buratai yace manufar taron shine domin sake yin nazari game da tsare tsaren tsaron da rundunar ta samar dangane da zaben shugaban kasa da na yan majalisun dokokin tarayya da na jihohi da za’ayi a ranar Asabar mai zuwa.

Bugu da kari Buratai ya bayyana damuwarsa ga yadda wasu yan siyasa ke siyasantar da umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar game da harbe duk wanda aka kama yana satar akwatin zabe, inda yace;

“Abin kunya ne ace mutumin dake neman takarar zama shugaban kasar Najeriya ya dinga tunzura Sojoji suyi ma umarnin shugaban kasa bore, mun sha fada matsayinmu a siyasa itace tsaya tsaka tsakiya, amma ba zamu lamunci tunzura Sojoji ga rashin biyayya ba.” Inji shi

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel