Gwamnatocin baya ne suka lalata tsarin aikin gwamnati - Buhari yayin rantsar da Sabbin Sakatarori

Gwamnatocin baya ne suka lalata tsarin aikin gwamnati - Buhari yayin rantsar da Sabbin Sakatarori

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati guda 8

- Ya horey su da su kawo gudummawa wajen magance matsalolin kasar

- Shugaban yace gwamnatin da ta shude ta taka rawar gani wajen lalata aiyukan gwamnati

Gwamnatocin baya ne suka lalata tsarin aikin gwamnati - Buhari yayin rantsar da Sabbin Sakatarori

Gwamnatocin baya ne suka lalata tsarin aikin gwamnati - Buhari yayin rantsar da Sabbin Sakatarori
Source: Facebook

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya rantsar da sabbin sakataren gwamnati 8 a fadar shi dake Abuja.

Takaitaccen bikin anyi shi ne kafin a fara taron zababbu na gwamnatin tarayya.

Sabbin zababbun daraktoci ne da aka zabe su don wakiltar jihohi 8 na kasar nan.

Sabbin sakatarorin sun hada da Oluwuyiwa Enitan na jihar Osun, Mohammed Dikwa na jihar Borno, Ajani Madaline ta jihar Delta da Festus Yesufu Daodu na jihar Nasarawa.

Sauran sun hada da Nnamdi Maurice Mbaeri jihar Imo, Bakari Wadinga jihar Adamawa, Babatunde Lawal jihar Legas da Ernest Afolabi Umakhihe na jihar Edo.

Yayin taya sabbin sakatarorin murna, Buhari yace zaben su da akayi ya taho da nauyi mai yawa.

Ya horey su dasu taimakawa gwamnati don ta shawo kan Matsalolin ta ta hanyar tabbatar da sabbin tsare tsaren ta.

GA WANNAN: CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi

Ya tabbatar da cewa gwamnatin da ta shude ce ta lalata aiyukan gwamnati, yace gwamnatin shi tayi alkawarin samun nasara a bangarori uku da suka da suka hada da tsaro, tattalin arziki da fada da rashawa.

Yace su maida hankali akan aiyukan su saboda shima zai maida hankali wajen tabbatar da walwalar su.

Yace: "Zan fara da taya ku murna. Kun dau rantsuwa ta sakatarorin gwamnatin tarayya. Wannan nasara ce da yakamata kuyi alfahari da ita. Kadan daga cikin yan Najeriya ne ke samun kaiwa matsayin nan. Na tabbatar da cewa kafin ku iso nan kun fuskanci kalubale masu yawa tare da sadaukarwa,"

"A yau ku da iyalanku na murnar kaiwa wannan matsayi. A yayin wannan murnar, inaso in tunatar daku rantsuwar da kuka dauka ta matsayin ku, tana tafe ne da nauyi mai yawa. A yanzu fiye da da, kasar mu na bukatar jajirtattu kuma kwararrun ma'aikatan gwamnati da zasu taimaka wajen shawo kan manyan matsalolin kasar mu.

A matsayinmu na 'yan siyasa muna habaka sabbin tsare tsare da kuma samar da alkibla ga kasar mu. Amma kuma nauyin aiwatar da tsare tsaren ya rataya ne a wuyan ma'aikatan gwamnati karkashin jagorancin sakatarorin gwamnati,"

"Nasan kunsan yanda gwamnatin da ta shude tayi amfani da mulki ta lalata aiyukan gwamnati."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel