Gamayyar kungiyar ma su sa-ido a zabe sun bayyana halin da Kano ke ciki

Gamayyar kungiyar ma su sa-ido a zabe sun bayyana halin da Kano ke ciki

- Kungiyar masu lura da zabe na cikin gida Najeriya sun tabbatar da cewa jihar Kano a shirye take don zabe

- Sun samo bayanin ne ta zagayen da sukayi a jihar kano da kewayenta

- Jami'an tsaro shirye suke don bada kariyar dukiyoyi da rayuka

Kungiyar masu lura da zabe na cikin gida wandanda INEC ta tantance a Kano sun hori yan uwan su da ke sauran garuruwa dasu kwantar da hankalin su cewa da garin yayi lafiya kuma da zaman lafiya.

Shugaban kungiyar, Comrade Friday Maduka, yayi kiran yayin jawabin kafin zabe ga manema labarai a Kano a ranar laraba.

"Sakamakon zagayen da mukayi a jihar, muna horan sauran abokan aikin mu da kada suji tsoro. Babu wata tashin tashina a Kano domin akwai kwanciyar hankali da lumana," inji Maduka.

Gamayyar kungiyar ma su sa-ido a zabe sun bayyana halin da Kano ke ciki

Rumfar zabe
Source: Twitter

Yace bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jihar, kungiyar ta amince da cewa cibiyoyin tsaro na jihar na shirye don samar da tsaro.

GA WANNAN: Bai kamata sojoji suyi aikin tsaro a zabe ba, na 'yansanda ne aikin - Babban Provost na hukumar

"Yanayin tsaron zai tabbatar da tsaron rayuka da kadarori yayi da bayan zabe a jihar, a don haka ne jihar Kano na zaune cikin lumana da kuma shirin zabe mai zuwa," inji shi.

Kamar yanda shugaban ya fada, INEC ma ta shirya ma zaben. Yayi kuma kira ga jami'an tsaro balle yan sanda dasu tsananta tsaro wajen kawo karshen bangar siyasa don tabbatar da zaman lafiya a jihar.

"Wadanda kesa kansu cikin aiyukan ashsha za a kamasu kuma su karbi hukuncin shari'a yanda ya kamata," inji shi

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel