Ina da tabbacin za a gudanar da zabe na gaskiya da adalci - Buhari

Ina da tabbacin za a gudanar da zabe na gaskiya da adalci - Buhari

- Shugaban kasa Buhari ya yi kira ga al'ummar Najeriya a kan su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'un su a babban zabe

- Bayan rarrashi shugaba Buhari ya nemi afuwar 'yan Najeriya sakamakon tasgaron da suka fuskanta a sanadiyar dage zabe a makon da ya gabata

- Buhari ya bayar da tabbacin sa ga al'ummar kasar nan wajen tabbatar da zabe na gaskiya da adalci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayin neman al'ummar Najeriya akan kada gwiwowin su su sanyaya sakamakon dage babban zabe, ya yi kira da su fito kwansu da kwarkwata domin kada kuri'un su a ranar Asabar, 23, ga watan Fabrairun 2019.

Ina da tabbacin za a gudanar da zabe na gaskiya da adalci - Buhari

Ina da tabbacin za a gudanar da zabe na gaskiya da adalci - Buhari
Source: Twitter

Cikin wani sabon bidiyo na rarrashi a jiya Talata, shugaban kasa Buhari yayi nemi afuwar al'ummar Najeriya sakamakon tasgaro da wahalhalu da suka fuskanta a sanadiyar dage babban zaben kasar nan.

Bidiyon shugaba Buhari yayin gabatar da jawaban sa ga al'ummar Najeriya cikin harshen Hausa

Kazalika shugaban kasar ya yabawa al'ummar Najeriya sakamakon juriyar su gami da hakuri inda ya sha alwashi tare da sake bayar tabbacin sa kan gudanar da zabe na gaskiya da adalci a fadin kasar nan.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta dage babban zaben kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya sa'a'i kadan gabanin gudanar sa.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Kwankwaso ya yiwa Atiku kamfe a jihar Legas

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, wani dan majalisar tarayyar kasar Amurka, Chris Smith, ya ce ba bu wani mai laifi sakamakon dage babban zaben kasar nan da ya wuce shugaban kasa Buhari da kuma makarraban sa.

Mista Smith yayin jaddada ikirarin sa ne cewar dole shugaba Buhari ya dora laifin dage zaben kasar nan a wuyan sa, ya kuma yi kira ga gwamnatin shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a ta sanya idanun lura kan sha'anin Najeriya kasancewar ta madubin dubawa a nahiyyar Afirka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel