Yanzu Yanzu: Yan Shi’a na zanga-zanga a ma’aikatar harkokin waje

Yanzu Yanzu: Yan Shi’a na zanga-zanga a ma’aikatar harkokin waje

- Mambobin kungiyar Shi’a sunyi zanga-zanga a ofishin ma’aikatar dake kula da harkokin waje

- Yan Shi'an na zanga-zangan ne a gaban masu aikin sa ido na zabe da suka zo daga kasashen ketare

Mambobin kungiyar yan uwa Musulmai na Shi'a sun yi zanga-zanga a harabar ma’aikatar dake kula da harkokin waje don jan hankulan kasashen ketare akan bukatarsu na ganin an saki shugaban kungiyar, Sheik Ibrahim El-zakzaky.

Mambobin kungiyar na amfani da daman yin zanga-zangan ne a gaban masu aikin sa ido na zabe da suka zo daga kasashen ketare.

Kimanin shekaru uku kenan da shugaban kungiyar ke tsare a bisa umurnin gwamnatin tarayya, duk da cewar wata kotun tarayya ta yi umurnin sakin sa.

An tsare shugaban Shi'an ne tare da uwargidansa bisa wasu zarge-zarge da suka hada da kisan kai, da kuma zargin tara jama'a ba bisa ka'ida ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati 8 (jerin sunaye)

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar Sunnah ta Najeriya mai suna Sunnah Group of Nigeria (SGN) ta zargi dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar da samun nasaba da kungiyar yan uwa Musulmi na Shi’a.

A wani jawabi da Shugaban kungiyar, Muntaka Kafinsoli, ya ake wa manema labarai a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu yayi zargin cewa dan takarar Shugaban kasar na PDP a yanzu haka yana neman alfarmar kuri’u daga wajen yan Shi’a.

Sai dai kungiyar ta gaza gabatar da wani kwakwaran hujja akan zargin da take yiwa tsohon mataimakin Shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel