Buhari bai yi kuskure ba, wanda ke son ransa ya guji satar akwatin zabe - Festus Keyamo

Buhari bai yi kuskure ba, wanda ke son ransa ya guji satar akwatin zabe - Festus Keyamo

- Festus Keyamo, ya jinjinawa shugaban kasa Buhari bisa hangen nesansa na yin wannan furucin da 'yan Nigeria ke kallo a matsayin ba dai-dai ba

- A wani taron kusoshi da shuwagabannin APC, Buhari ya yi barazanar kisa ga duk wanda aka cafke ya saci akwati a zabukan kasar da ke gabatowa

- Keyamo ya ce furucin shugaban kasar bai sabawa dokar kasa ba. Yana mai karfafawa Buhari guiwa akan ci gaba da furta irin wadannan kalamai

A wani taron kusoshi da shuwagabannin kungiyoyin jam'iyyar APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanar da wata barazana ta kisa ga duk wanda aka cafke ya saci akwati a zabukan kasar da ke gabatowa.

"Ka saci akwatin zabe, ka biya da rayuwarka," shi ne furucin da shugaban kasar ya yi, wanda da yawan 'yan Nigeria da suka hada da jam'iyyar adawa ta PDP, suka yi kalubalanci shugaban kasar tare da bayyana furucin a matsayin "son zubar da jinin 'yan Nigeria ba gaira ba dalili."

Sai dai da ya ke tsokaci kan furuchin shugaban kasar a wani shirin talabijin na Channels TV, mai taken 'VERDICT', babban lauya a Nigeria, Festus Keyamo, ya jinjinawa shugaban kasa Buhari bisa hangen nesansa na yin wannan furucin da 'yan Nigeria ke kallo a matsayin ba dai-dai ba.

KARANTA WANNAN: PDP ba ta isa ta hana mu bin umurnin Buhari ba - Rundunar soji ta yiwa Atiku martani

Buhari bai yi kuskure ba, wanda ke son ransa ya guji satar akwatin zabe - Festus Keyamo

Buhari bai yi kuskure ba, wanda ke son ransa ya guji satar akwatin zabe - Festus Keyamo
Source: Depositphotos

Ya yi nuni da cewa furucin shugaban kasar bai wani saba da dokar kasa ba. Yana mai cewa zai kasance mai karfafawa Buhari guiwa akan ci gaba da furta irin wadannan kalamai.

Ya ce: "Na saurari kalaman na sa, na kuma nazarci tsokacin da 'yan Nigeria ke yi akan furucin na shugaban kasar, musamman ma matsayar jam'iyyar adawa. Sai dai bari na sanar da ku wani abu, babu wani laifi a furucin Buhari, duk abunda ya fada dai-dai ne ko a doka.

"Mutane na magana ne kawai ba tare a duba gaskiyar maganar a hukumance ba. Dan ta'adda ne kamar dan fashi ne, ko mai kisan kai, wanda sam bai da tausayi ko imani. Doka ta tanadar da cewa idan har aka samu d'an ta'adda yana aikata laifin da zai iya jefa rayukan jama'a cikin hatsari, to a harbe shi nan take."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel