Labari cikin hotuna: Taron majalisar zartarwa a karkashin jagorancin Buhari

Labari cikin hotuna: Taron majalisar zartarwa a karkashin jagorancin Buhari

A yanzu haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kammala jagorantar zaman majalisar zartarwa, da ta kunshi ministocin gwamnatinsa, mashawartarsa, manyan ma’aikatan gwamnatin tarayya da ire irensu, a fadar gwamnatin Najeriya Aso Rock Villa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan zama ana yinsa ne dama a ranar Laraba na kowanne mako, kuma shine zai zamo zama na karshe da za’ayi kafin zaben 2019, wanda aka dagashi daga ranar 16 ga watan Feburairu zuwa ranar 23 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Wani kasurgumin mai garkuwa da mutane ya shiga hannun hukuma a Katsina

Labari cikin hotuna: Taron majalisar zartarwa a karkashin jagorancin Buhari

Buhari
Source: Twitter

Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnati, Boss Mustapha, shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari, shugabar ma'aikatan Najeriya Winnfired Eyo Ita.

Ana gab da zaman majalisar zartarwar na yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar sabbin manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnati, wanda suka hada Olumuyiwa Abel, Mohammed Dikwa, Magdalene Ajani, da Festus Daudu.

Sauran manyan sakatarorin ma’aikatun gwamnatin da shugaba Buhari ya rantsar dasu a ranar Laraba 20 ga watan Feburairu sun hada da Maurice Mbaeri, Bakari Wadinga, Babatunde Lawal da Ernest Umakhihe.

Labari cikin hotuna: Taron majalisar zartarwa a karkashin jagorancin Buhari

Taron majalisar zartarwa
Source: Twitter

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umari ma’aikatar kudi ta Najeriya ta tabbata ta biya albashin ma’aikata na watan Feburairu domin su rage radadin zirga zirgar da suka yi sakamakon dage zaben 2019.

Ministan watsa labaru, Lai Muhammed ne ya bayyana haka bayan kammala taron majalisar zartarwa, inda yace a yanzu haka gwamnatin tarayya ta fara biyan albashin ma’aikatanta daga ranar Talata, 19 ga watan Feburairu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel