Shugaba Buhari ya umarci a biya Ma’aikatan Gwamnati albashin Fubairu

Shugaba Buhari ya umarci a biya Ma’aikatan Gwamnati albashin Fubairu

- Buhari ya bada umani a biya albashi saboda dage zaben shugaban kasa da aka yi

- Shugaban kasar ya bada umarni a fitar da albashin wannan wata cikin gaggawa

- An bayyana wannan ne bayan taron Majalisar zartarwa ta FEC da aka yi dazu nan

Shugaba Buhari ya umarci a biya Ma’aikatan Gwamnati albashin Fubairu

Buhari ya bada umarni a biya albashin watan nan domin rage fushin dage zabe
Source: Twitter

Mun samu labari dazu nan cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni ga manyan jami’an gwamnati da su yi maza su biya ma’aikatan da ke aiki a karkashin gwamnatin tarayya albashin su na watan nan da ake ciki.

Shugaban kasar ya bada wannan umarni ne a dalilin dakatar da zabe da aka yi a makon da ya gabata. Hakan zai bada dama ga wasu ma’aikatan da su kayi ta jigila a karshen makon jiya da su samu sa’ida a daidai karshen watan nan.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya rantsar da sabbin manyan Sakatarorin Gwamnati

Ministan yada labarai da kuma al’adu na gwamnatin Najeriya watau Alhaji Lai Mohammed ya bayyanawa menema labarai wannan ba da dadewa ba. Ministan yayi wannan jawabi ne bayan taron FEC na ministoci da aka yi.

Wannan karo za a biya albashi ne kafin lokacin da aka saba inji ministan. A baya dai gwamnati na biyan albashin ma’aikata ne a ranar 25 na kowane wata. Gwamnati ta sabawa wannan tsari a watan nan saboda dage zabe da INEC tayi.

Kawo yanzu dai abin da mu ka samu labari kurum kenan daga bakin ministan wanda ya gana da ‘yan jaridar da ke cikin fadar shugaban kasa bayan ministoci da sauran kusoshin gwamnati sun yi zaman FEC da aka saba yi a duk mako.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Online view pixel