Barayin akwati daidai su ke da makiyan kasa a wurin mu - Buratai

Barayin akwati daidai su ke da makiyan kasa a wurin mu - Buratai

- Shugaban sojin Najeriya yace zasu dau duk mai zagon kasa ga damokaradiyyar mu a matsayin makiyi

- Shugaban yace shirye suke don magance bangar siyasa

- Sojin zasuyi aiki damasu ruwa da tsaki, kungiyoyi da cibiyoyin tsaro don magance zagon kasa ga damokaradiyyar mu

Shugaban sojin Najeriya Lt Col Tukur Buratai yace masu zagon kasa Ga zaben Najeriya za a dauke su a matsayin makiyan Najeriya.

Buratai yayi maganar ne a hedkwatar sojin Najeriya dake Abuja, yayin taro da manyan hafsin sojin.

Yace: "Hadin kan yan Najeriya yafi komai,don haka duk wanda ke zagon kasa ga damokaradiyyar mu ta hanyar shiga lamarin zaben mu muna ganin shi ne a matsayin makiyin kasar nan kuma dole mu hukunta shi,"

"Bangar siyasa, satar akwatin zabe, Samun kayan zabe da sauran laifuka makamantan su da kuma sabbaba hargitsi bayan zabe,"

Barayin akwati daidai su ke da makiyan kasa a wurin mu - Buratai

Buratai
Source: Depositphotos

"Wadannan abubuwan zasu yi ma kasa illa idan suka yawaita tare da kawo asarar rayuka da dukiyoyi," inji Buratai.

Yace abubuwa makamantan hakan da suka faru a zaben da ya gabata ba a tsara su ba kuma yan siyasa ne suka assasa kuma dole ne sojin su dau mataki.

GA WANNAN: Gargadin karshe da APC ta yiwa Turawan Yamma: Kuji da matsalolinku na tattalin arziki

Buratai yace: "A wannan lokacin, sojin Najeriya zasu dau hanyoyin gyara don hana faruwar hakan nan gaba."

Yace sojin dole suyi aiki da masu ruwa tsaki, kungiyoyi da cibiyoyi don hana aika aika daga kowanne mutum, kungiya ko kuma jam'iyyun siyasa don zagon kasa ga damokaradiyyar mu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel