CUPP ta zargi APC da yin amfani da DSS don yiwa 'yan jam'iyyar adawa labe

CUPP ta zargi APC da yin amfani da DSS don yiwa 'yan jam'iyyar adawa labe

Hadakan jam'iyyun adawa CUPP ta yi ikirarin cewa hukumar 'yan sandan farar hula na DSS tana labe a kan hirar tarho na jiga-jigan mambobin jam'iyyun siyasa na adawa a kasar.

CUPP ta ce ana sauraron hirar tarho ne jam'iyyun adawan ne saboda jam'iyyar All Progressives Congress ta samu abubuwan da za tayi amfani da su a zabe da ke tafe.

Mai magana da yawun CUPP na kasa, Imo Ugochinyere ne ya yi wannan zargin cikin wata sanarwa da ya bawa manema labarai a ranar Laraba.

CUPP ta zargi APC da yin amfani da DSS don yiwa 'yan jam'iyyar adawa labe

CUPP ta zargi APC da yin amfani da DSS don yiwa 'yan jam'iyyar adawa labe
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Ya ce, "munyi matukar mamaki da bakin cikin gano cewa jam'iyyar APC tana amfani da gurabatattun hukumomin tsaro domin sauraron hirar da shugabanin mu keyi a wayar tarho domin gano shirye-shiryen mu na zabe.

"Jam'iyyun adawa sun gano cewa jam'iyyar APC ta dade tana kuste tare da sauroron hirar wayar targo da shugabanin mu keyi ta hanyar amfani da DSS.

"Wannan abin kunyar ya matukar bata mana rai kuma hakan ya nuna gwamnati mai ci yanzu tana jin tsoron fadi zabe fiye da kowa."

Ugochinyere ya yi kira ga shugabanin CUPP su dena amfani da wayar tarho domin tattauna muhimman bayanai sai dai su rika haduwa suyi magana ko suyi amfani da Whatsapp.

Ya kara da cewa, "Muna kira ga mambobin mu su rika amfani da WiFi domin hira a Whatsapp domin hakan zai rage yiwuwar ayi musu kutse cikin hirar da su keyi.

"Ga hukumomin tsaron du suka bari gwamnati ke amfani da su muna kira garesu su dena yi mana kutse cikin hirar wayar tarho da sauran sakonnin mu su mayar da hankali akan ayyukan kasa masu muhimmanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel