Gobara ta kone shaguna 31 a kasuwar Sheikh Gumi a Kaduna

Gobara ta kone shaguna 31 a kasuwar Sheikh Gumi a Kaduna

Shaguna 31 da kayayakin abinci na miliyoyin naira ne suka kone a gobarar da ta faru a ranar Laraba a babban kasuwan Sheikh Gumi da ke bakin Dogo a garin Kaduna a jihar Kaduna.

An gano cewar wutar ta fara ci ne misalin karfe 2 na daren Laraba a lokacin da mafi yawancin masu shagunan suke gidajensu.

Har yanzu ba a kamalla sanin dalilin afkuwar gobarar ba sai dai wasu 'yan kasuwan sun ce matsalar wutan lantarki ne.

Gobara ta kone shaguna 31 a kasuwar Sheikh Gumi a Kaduna

Gobara ta kone shaguna 31 a kasuwar Sheikh Gumi a Kaduna
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

Daily Trust ta ruwaito cewa galibi shagunan da suka kone na masu sayar da masara ne da rogo da ke Birnin Kudu a bakin Dogo a kasuwar.

A yayin da majiyar Legit.ng ta ziyarci wurin da gobarar ya faru, sun gano mutane da dama da suka zo jajantawa masu shagunan.

Shugaban kungiyar masu sayar da rogo a bakin Dogo, Alfa Hussaini ya ce 'yan kasuwar suna bukatar tallafi.

"Munyi asara sosai sakamakon gobarar, Allah ne kadai zai iya taimaka mana saboda ba mu san daga inda wutar ta fara ba. Shaguna 31 ne suka kone kuma kana iya ganin yawancin masu shagunan mata ne," inji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta tallafawa wadanda suka rasa kayayakin su sakamakon gobarar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel