Ana gab da zabe: Yar takarar shugaban kasa ta janye, ta mara wa Atiku baya

Ana gab da zabe: Yar takarar shugaban kasa ta janye, ta mara wa Atiku baya

Rahotanni sun kawo cewa Eunice Atuejide, yar takaran kujeran shugaban kasa a jam’iyyar National Interest Party (NIP), ta janye daga zaben shugaban kasa da aka daga kwanan nan.

A wani jawabi da ta gabatar a safiyan ranar Laraba, Misis Atuejide na jam’iyyar NIP tace ta janye daga takarar ne saboda dama ta shirya kawo karshen fafutukarta ne a ranar 16 ga watan Fabrairu.

A wata da ya gabata ne, ta bayyana cewa shugaban kasa Buhari na fama da rashin lafiyan kwakwalwa sannan baya da cikakken lafiya da zai iya cigaba da gudanar da aikin ofis, inda tace ta dau matakin takara ne don “tsayar” da shi.

A wani hira tare da Premium Times, lauyan ta bayyana dalilin da yasa zata yi amfani da matakan kotu don hana rantsar da shugaban kasa Buhari har idan ya lashe zabe.

Ana gab da zabe: Yar takarar shugaban kasa ta janye, ta mara wa Atiku baya

Ana gab da zabe: Yar takarar shugaban kasa ta janye, ta mara wa Atiku baya
Source: Twitter

A jawabinta na ranar Laraba, Misis Atuejide ta bada dalilan bayyana goyon baya ga Mista Abubakar, wanda daya daga cikin dalilan ya kasance irin zabin da yayi na mataimakin shugaban kasa.

Janyewar Misis Atuejide ya cigaba da rage adadin mata da ke takaran kujeran shugaban kasa.

Har ila yau, fiye da mata biyar ne suka janye daga takaran shugaban kasa ko da yake takardan zabe na dauke da sunayensu. Kimanin jam’iyyu guda 73 da yan takaransu ne zasu kasance akan takardan zabe na shugaban kasa, hade da sunayen wadanda suka janye kwanan nan, inji INEC.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati 8 (jerin sunaye)

Wassu daga cikin mataye da suka janye daga takaran sannan sunayensu zasu kasance akan takardan zaben sun hada da tsohuwar ministan ilimi, Oby Ezekwesili, da Rabia Cengiz na jam’iyyar National Action Council (NAC) sannan kuma a halin yanzu Misis Atuejide.

Babu macce da ta lashe kujerar shugabancin kasa, mataimakin shugaban kasa ko zababben gwamna a cikin shekaru 19 na damokardiyyan Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel