Atiku ya sha alwashin lashe zaben 2019

Atiku ya sha alwashin lashe zaben 2019

Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana kwarin gwiwar cewa shi ne zai lashe zaben shugaban kasa da za'a yi ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya ce caccakar mulkin jam’iyyar PDP na tsawon shekaru 16 cewa ba ta yi komai ba soki burutsu ne.

Ya bayyana hakan ne a wurin taron majalisar koli na jam’iyyar PDP da aka yi a hedkwatarta da ke Wadata Plaza a Abuja.

Taron na su, ya duba tasirin dage zaben makon jiya da kuma shan alwashin komawa bakin dagar kamfen.

Atiku ya sha alwashin lashe zaben 2019

Atiku ya sha alwashin lashe zaben 2019
Source: UGC

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki, a lokacin da yake jawabi ya nuna tamkar Atiku shugaban kasa ne mai jiran gado da yardar Allah bayan zaben ranar Asabar mai zuwa, inda ya nuna gazawar gwamnati Buhari ta APC zai ba su dama su lashe zaben.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda da dama suka ji rauni a kamfen din APC a Kwara

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar Sunnah ta Najeriya mai suna Sunnah Group of Nigeria (SGN) ta zargi dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar da samun nasaba da kungiyar yan uwa Musulmi na Shi’a.

A wani jawabi da Shugaban kungiyar, Muntaka Kafinsoli, ya ake wa manema labarai a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu yayi zargin cewa dan takarar Shugaban kasar na PDP a yanzu haka yana neman alfarmar kuri’u daga wajen yan Shi’a.

Sai dai kungiyar ta gaza gabatar da wani kwakwaran hujja akan zargin da take yiwa tsohon mataimakin Shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel