Sojojin Saman Najeriya sun lalata sansanin Boko Haram a Arboko

Sojojin Saman Najeriya sun lalata sansanin Boko Haram a Arboko

- Dakarun Sojojin Saman Najeriya NAF sun yi nasarar lalata sansanin 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram da ke kauyen Arboko a jihar Borno

- Rundunar NAF tayi amfani da jirgin yaki na Alfa Jet ne wurin yin luguden wuta a sansanin 'yan ta'addan bayan samun bayan sirri daga ISR

- Rundunar Sojojin saman NAF tare da dakarun sojin kasa sun ce ba za tayi kasa a gwiwa ba har sai sun ga bayan dukkan 'yan ta'addan da su kayi saura a yankin Arewa maso Gabashin kasar nan

Sojojin Saman Najeriya sun lalata sansanin Boko Haram a Arboko

Sojojin Saman Najeriya sun lalata sansanin Boko Haram a Arboko
Source: Twitter

A yau Laraba ne rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ta ce dakarunta sun lalata wani sansanin 'yan kungiyar Boko Haram tare da halaka 'yan ta'adda mas yawa a garin Arboko na jihar Borno.

Kakakin rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola yace an kai samamen ne a ranar 18 ga watan Fabrairu a inda jirgin yaki na Alpha Jet tare taimakon na'urarar tattaro bayanan sirri na ISR ya taimakawa rundunar sojin na 82 Brigade na sojin Najeriya kai harin.

DUBA WANNAN: Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Ya ce a yayin kai farmakin jirgin ISR ya gano wani wuri da gungun 'yan ta'adda suka taru a kauyen Arboko kuma nan take ya sanar ya bawa Alpha Jet umurnin yin luguden wuta a kan sansanin wadda hakan ya lalata dukkan gine-gine da ke sansanin tare da kashe 'yan ta'adda da dama.

Ya kara da cewa NAF, tare da sauran dakarun sojoji da ke yaki a doron kasa ba za suyi kasa a gwiwa ba har sai sun ga bayan dukkan sauran 'yan ta'addan da suka rage a yankin na Arewa maso Gabashin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel