Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati 8 (jerin sunaye)

Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati 8 (jerin sunaye)

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya rantsar da sabbin Sakatarorin Gwamnatin Tarayya.

Shugaban kasar ya rantsar da su ne a ranar Laraba, a majalisar fadar shugaban kasa. Wannan na zuwa ne Jim kadan kafin a fara zaman majalisar na mako.

Sabbin sakatarorin sun hada da Olumuyiwa Abel, Mohammed Dikwa, Magdalene Ajani, Festus Daudu, Maurice Mbaeri, Bakari Wadinga, Babatunde Lawal da Ernest Umakhihe.

Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati 8 (jerin sunaye)

Yanzu Yanzu: Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin gwamnati 8 (jerin sunaye)
Source: Twitter

Yayinda yake taya sabbin sakatarorin murna, shugaba Buhari yace waannan rantsuywa da suka yi ya zama wani babban kaya akansu.

Ya bukaci da su taimakawa gwamnati wajen shawo kan matsalolinta ta hanyar bin ka’idojin manufofinta.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda da dama suka ji rauni a kamfen din APC a Kwara

A wani lamari na daban, mun ji cewa babban sakataren yada labarai na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Kola Ologbondiyan ya ce wasu daga fadar shugaban kasa da jam'iyyar APC za suyi duk mai yiwuwa domin ganin Atiku Abubakar ya lashe zaben shugabancin kasa.

A wata hira da The Tribune ta wallafa a ranar Laraba 20 ga watan Fabrairu, Ologbondiyan ya ce ya yi imani cewa jam'iyyar PDP ce za ta lashe zaben shugaban kasa da wasu zabukka a jihohin Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel