Yanzu-yanzu: An kashe shugaban jam'iyyar APC a jihar Imo

Yanzu-yanzu: An kashe shugaban jam'iyyar APC a jihar Imo

Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan daban siyasa ne sun harbe shugaban jam'iyyar Progressives Congress chairman na mazabar Logara/Umuohiagu da ke karamar hukumar Ngor Okpala na jihar Imo har lahira.

Punch ta ruwaito cewar an kashe Ifeanyi Ozoemena ne a daren jiya Talata sa'o'i biyu bayan ya kammala jagorancin taron jam'iyyar APC a mazabarsa inda suke shirin tunkarar zaben shugabancin kasa da na 'yan majalisun tarayya a ranar Asabar mai zuwa.

A cewar wadanda abin ya faru a idanusu, an harbe shugban jam'iyyar ne a gaban iyalansa.

Yanzu-yanzu: An kashe shugaban jam'iyyar APC a jihar Imo

Yanzu-yanzu: An kashe shugaban jam'iyyar APC a jihar Imo
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Mataimakin shugaban kungiyar Logara Development Union, Martin Opara ta tabbatar da kisar inda ya ce dukkan garin ya girgiza bisa mummunan lamarin.

Ya ce irin wannan kisar na siyasa ba ta taba faruwa a garin ba kuma ya bukaci hukumomin tsaro suyi gaggawan binciko wadanda suka aikata lafin tare da hukunta su.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Dasuki Galadanci ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce tuni an dauke gawar marigayin.

A cewar kwamishinan, yan bindigan da suka kashe shugaban na APC sun taho ne a cikin mota kirar SUV .

Shugaban 'yan sandan ya ce, "an fara gudanar da bincike a kan lamarin. Yan bindigan da suka harbe shi tun taho ne a mota kirar SUV.

"Lamarin ya faru ne yayin da suke shirin tunkarar babban zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu da za ayi a ranar Asabar mai zuwa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel