Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

- Kakakin jam'iyyar PDP na kasa, Kola Ologbondiyan ya yi ikirarin cewa wasu 'yan APC za su taimakawa Atiku Abubakar ya lashe zaben shugabancin kasa na 2019

- Ologbondiyan ya ce jam'iyyar PDP tayi imanin cewa ita ce za ta lashe zaben shugaban kasa da wasu zabukkan da za ayi a sassan kasar nan

- Jigon na PDP ya ce rashin cika alkawurra da gwamnati mai ci yanzu ba tayi ba zai sanya 'yan Najeriya su ki jefa wa Buhari kuri'a a babban zaben 2019

Babban sakataren yada labarai na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Kola Ologbondiyan ya ce wasu daga fadar shugaban kasa da jam'iyyar APC za suyi duk mai yiwuwa domin ganin Atiku Abubakar ya lashe zaben shugabancin kasa.

A wata hira da The Tribune ta wallafa a ranar Laraba 20 ga watan Fabrairu, Ologbondiyan ya ce ya yi imani cewa jam'iyyar PDP ce za ta lashe zaben shugaban kasa da wasu zabukka a jihohin Najeriya.

DUBA WANNAN: Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP

Wasu na kusa da Buhari za su taimakawa Atiku samun nasara - PDP
Source: UGC

Ya ce rashin cika alkawurran farfado da tattalin arziki, yaki da rashawa da yaki da ta'addanci da gwamnatin APC ta gaza zai sanya 'yan Najeriya su juya wa Buhari baya a yayin zaben 2019.

"... Muhammadu Buhari ya gaza cika alkawarin da ya dauka na farfado da tattalin arziki, yaki da rashawa da yaki da ta'addanci. A maimakon bunkasa tattalin arzikin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mika masa, saboda tsabar rashin kwarewa Buhari ya ruguza tattalin arzikin Najeriya.

"Duk al'amurran rayuwa sun tabarbare, wannan kadai dalili ne da zai sanya 'yan Najeriya su juya wa Buhari baya a yayin zaben 2019," inji Ologbondiyan.

"A bangaren yaki da ta'addanci kuwa, Shugaba Buhari ya gaza tabbuka komai hakan yasa wasu mazauna jihohin da abin ya shafa suke hijira zuwa Jamhuriyar Nijar. A fanin yaki da rashawa kuwa, kawai mutum ya dubi wadanda ke kewaye da shugaban kasa zai gane gaskiya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel