Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda da dama suka ji rauni a kamfen din APC a Kwara

Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda da dama suka ji rauni a kamfen din APC a Kwara

Rahotanni da ke zuwa mana daga TVC yayi ikirarin cewa wasu yan iska sun kashe mutum daya yayinda suka raunata mutane da dama a wajen kamfen din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da ke gudana a jihar Kwara.

Legit.ng ta samu labarin cewa an daura alhakkin harin akan babbar jam’iyyar adawa wato, Peoples Democratic Party (PDP).

Television Continental (TVC) ta ruwaito cewa kamfen din ya zama rikici ne a Ojoku, jihar Kwara, yayinda jam’iyyar APC da PDP ke nunawa juna yatsa a matsayin wanda ya haddasa rikicin.

Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda da dama suka ji rauni a kamfen din APC a Kwara

Yanzu Yanzu: An kashe mutum 1 yayinda da dama suka ji rauni a kamfen din APC a Kwara
Source: Depositphotos

Yayinda APC ta daura alhakin arin akan PDP amma PDP ta karyata ikirarin inda tace maharan mambobin APC ne ba nata ba.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa hafsan rundunar sojin kasa Laftanal Janar Tukur Buratai, ya mayar da martani ga wata sanarwa da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fitar, na umurtar rundunar sojin da ta bijirewa umurnin Buhari na daukar mummunan mataki ga barayin akwatunan zabe.

KU KARANTA KUMA: Kotu za ta saurari karan da ke neman a hana Atiku takara bayan zaben Shugaban kasa

TY Buratai, wanda ya ce sanarwar Atiku abun takaici ce, kasancewar ya taba rike babban mukami a gwamnatin kasar kuma ya san cewa rundunar soji da ma duk jami'an tsaro, na bin umurnin babban kwamandan rundunar sojin kasar ba tare da neman ba'asi ko turjiya ba, ya ce za su bi umurnin Buhari ba tare da wata tankiya ba.

Da wannan, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya janye wannan sanarwar ta sa tare da kuma baiwa rundunar hakuri akan yunkurinsa na dakatar da ita daga bin umurnin da dokar kasar ta tanadar mata.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel