PDP ba ta isa ta hana mu bin umurnin Buhari ba - Rundunar soji ta yiwa Atiku martani

PDP ba ta isa ta hana mu bin umurnin Buhari ba - Rundunar soji ta yiwa Atiku martani

- TY Buratai ya gargadi Atiku Abubakar da ya kauracewa shiga harkokin da ya shafi rundunar sojin kasar

- Buratai ya jaddada cewa rundunar za ta bi umurnin da Buhari ya bayar na daukar mummunan mataki akan duk wanda aka kama ya saci akwatin zabe

- Ya ce rundunar soji na bin umurnin da Buhari ya bayar ba tare da haufi ba kasancewar babban kwamandan rundunar soji na kasar

Hafsan rundunar sojin kasa Laftanal Janar Tukur Buratai, ya mayar da martani ga wata sanarwa da dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fitar, na umurtar rundunar sojin da ta bijirewa umurnin Buhari na daukar mummunan mataki ga barayin akwatunan zabe.

TY Buratai, wanda ya ce sanarwar Atiku abun takaici ce, kasancewar ya taba rike babban mukami a gwamnatin kasar kuma ya san cewa rundunar soji da ma duk jami'an tsaro, na bin umurnin babban kwamandan rundunar sojin kasar ba tare da neman ba'asi ko turjiya ba, ya ce za su bi umurnin Buhari ba tare da wata tankiya ba.

Da wannan, ya bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya janye wannan sanarwar ta sa tare da kuma baiwa rundunar hakuri akan yunkurinsa na dakatar da ita daga bin umurnin da dokar kasar ta tanadar mata.

KARANTA WANNAN: Kar ku kashe barayin akwatunan zabe - Ortom ya gargadi DSS, Rundunar soji da 'yan sanda

PDP ba ta isa ta hana mu bin umurnin Buhari ba - Rundunar soji ta yiwa Atiku martani

PDP ba ta isa ta hana mu bin umurnin Buhari ba - Rundunar soji ta yiwa Atiku martani
Source: Depositphotos

Da ya ke jawabi a wani taron manyan jami'an rundunar sojin, da suka hada da PSO, GOC da kuma BC, domin tattauna shirye shiryen tarbar zaben kasar da za a gudanar a ranar Asabar, Buratai ya gargadi 'yan siyasa da magoya bayansu, da su kauracewa shiga hurumin karfin ikon rundunar soji, yana mai cewa duk wanda rundunar ta kama to kuwa za su dau mataki bisa umurnin da shugaban kasa Buhari ya ba su.

Duk da cewa bai ambaci sunan tsohon mataimakin shugaban kasar kai tsaye ba, amma bayanansa sun tafi kai tsaye ne ga sanarwar da dan takarar shugabancin kasar karkashin jma'iyyar PDP ya fitar.

Hafsan rundunar sojin ya bayyana cewa za a janje duk wasu jami'an soji da ke tsaron lafiyar janar-janar na soji musamman wadanda suka koma harkokin siyasa, saboda a cewarsa babu wani dan siyasa da za a rinka gadinsa har zuwa bayan zaben.

Ya gargadi jami'an sojin da su kauracewa sa hannu a harkokin siyasa, yana mai cewa duk mai sha'awar shigar siyasa to ya yi murabus kafin ranar Juma'a, 22 ga watan Fabreru.

Cikakken labarin yana zuwa..

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel