Da kyau: An damke yan bangan siyasa 950 a jihar Kano

Da kyau: An damke yan bangan siyasa 950 a jihar Kano

Hukumar yan sandan jihar Kano ta damke wasu mutane 950 da ake zargi da bangan siyasa cikin kwanaki 9 da suka gabata.

Kwamishanan yan sandan jihar Kano, Wakili Mohammed, ya bayyana hakan ne ranan Talata da kwamitin zaman lafiya Kano suka kai masa ziyara. Ya ce an damke yan bangan siyasan ne a wurare daban-daban a fadin jihar.

Daga cikin yan daba 950 da aka kama, 750 na kurkuku a yanzu yayinda ake sauraron gurfanarsu a kotu.

Wakili yace: "Muna gudanar da hare-hare a shahrarrun wurare kuma muddin muka damke ka kuma aka tabbatar da cewa kai dan daba ne, babu wanda zai karbi belinka,"

Hukumar yan sanda ba jam'iyyar siyasa bace, kuma idan jam'iyya ce, to jam'iyyata ce. Na amince na matsayarku, wacce itace zaman lafiya. Kuna da goyon bayana, saboda abunda kuka tsayawa shine ginshikin cigaban kasa."

KU KARANTA: Zaben 2019: Ina kira ga jama'ata sun fito su zabi Buhari - Dan takaran gwamna, Salihu Takai

A bayan mun kawo muku rahoton cewa sabon kwamishinan Yansandan jahar Kano, Muhammad Wakili ya bayyana manufarsa ta yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi a jahar Kano, koda kuwa hakan zai yi sanadiyyar salwantar rayuwarsa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wakili ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da cibiyar yan jaridu ta kai masa a ofishinsa dake garin Kano a ranar Talata, 19 ga watan Feburairu, inda ya bayyana shaye shaye a matsayin ummul haba’isun duk wasu laifuka da ake aikatawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel